Ina Cikin Tashin Hankali Tunda Alhaji Sani Ya Maka Ni A Gaban Kotu – Rarara
- Katsina City News
- 04 Feb, 2024
- 715
Jaridar Mikiya
Mawaƙi Dauda Adamu Abdullahi, wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana irin tashin hankali, da rashin sukunin da ya tsinci kansa, sakamakon ƙarar da Fitaccen Ɗan Jaridar nan, Alhaji Sani Ahmad Zangina ya shigar da shi, a gaban Babbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke Lafia, a jihar Nasarawa.
Bayanin yanayin da ya tsinci kan nasa kuma, na ƙunshe ne ta cikin ƙarar da ya ɗaukaka, kan umarnin da Kotun Majistirin ta bayar, a ranar 8 ga watan Janairun da ya gabata, wanda ke buƙatar ya bayyana a gabanta, a ya yin zaman shari’ar da Kotun ta gudanar, da safiyar jiya (Juma’a), 2 ga watan Fabrairu.
Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya maka Rarara a gaban Kotu ne dai, tun a ranar 1 ga watan Nuwamban 2023, ta cikin ƙunshin ƙara mai lamba : CM1LF/73/2023, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya jawo tunzuri a tsakanin al’umma, ya yin wani taron Manema Labarai da ya gabatar, a ɗakin taro na Bristol Hotel, da ke birnin Kano, ranar 27 ga watan Octoban 2023, bayan da ya zargi gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da damalmala al’amuran ƙasar nan, kafin miƙata ga shugaban ƙasa na yanzu, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Umarnin Rarara ya bayyana a gabanta, da Kotun Majistirin ta bayar, duk da sukar rashin huruminta na sauraron ƙarar da Lauyoyinsa su ka bayyana ne kuma, ya sanya Rararan garzayawa Babbar Kotun Jihar Nasarawa, da ke Doma, tare da roƙon Kotun da ta jingine wancan umarni na Kotun Majistiri, haɗi da umartarta da ta dakatar da sauraron waccar shari’a, har sai Babbar Kotun ta bayyana matsayarta, kan ƙarar da Rararan ya ɗaukaka.
Ta cikin ƙarar mai lamba: NSD/LF/10M/2024, Lauyoyin Rararan, da su ka haɗarda, A.I. Ma’aji; C.D. Usman; G.A. Badawi; M.I. Muhammad; S.Z. Abbas, S.S. Yakubu, sun bayyana cewar, wanda su ka ɗaukaka ƙara akansa na farko (Alhaji Sani Ahmad Zangina), da wacce su ke ƙara ta biyu (Mai Shari’a Mariam Nadabo, Ta Kotun Majistiri mai lamba 1), sun yi kuskure kan abinda su ka aikata, duba da cewar, Rararan ya furta abin da ake zarginsa da shi ne, a jihar Kano, amma aka maka shi ƙara a Kotun da ke Lafia, a jihar Nasarawa, baya ga rashin sanayya ta zahiri, da ke tsakaninsa da Alhaji Sani Ahmad Zanginan da ke ƙarar tasa, amma saboda yi wa shari’a gurguwar fahimta, Mai Shari’a Mariam Nadabo ɗin ta ɓata muhimman lokacin da Kotu ke da shi, wajen sauraron wannan shari’a da ke kamanceceniya da shiririta, ko wasan yara.
Ka zalika, saɗara ta bakwai cikin ƙarar da Rararan ya ɗaukaka, mai ɗauke da kwanan watan 30 ga watan Janairun da ya gabata, ta zargi Alhaji Sani Ahmad Zanginan da yunƙurin yin amfani da Rararan wajen samun ɗaukaka, ko yin suna.
Ya yin da saɗara ta 12 cikin ƙunshin ɗaukaka ƙarar kuwa, ta bayyana irin tashin hankalin da Rararan ya tsinci kansa, tun bayan shigar da shi ƙarar da Alhaji Sani Ahmad Zanginan ya yi.
Rarara yace, ya gudanar da taron Manema Labarai ne kawai, game da halin da siyasar ƙasar nan ke ciki, musamman ma Jam’iyyarsa ta APC, amma kwatsam ya yi tozali da takardar sammacin da Alhaji Sani Ahmad Zangina ɗin ya shigar da shi ƙara, wanda a cewarsa, ko kaɗan basu san juna a zahiri ba.
Tuni dai Babbar Kotun jihar Nasarawa ta sanya ranar, 12 ga watan Fabrairun da mu ke ciki, domin sauraron ƙarar da Rararan ya ɗaukaka, ya yin da a gefe guda, Kotun Majistirin da ke Lafia, ta sanya ranar 9 ga wata, domin cigaba da sauraron shari’ar.