Tun bayan Hare-haren 'Yan bindiga: Mutanen Shimfida sun Koka akan mawuyacin halin da suke ciki...
- Katsina City News
- 29 Jan, 2024
- 442
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Al'umar garin Shimfida dake karamar hukumar Jibiya da akai hasashen Mutum fiye da Dubu Biyar na rayuwa a cikinsa sun koka akan mawuyacin halin da suke ciki na rashin Asibiti, Makarantun Islamiyya da na Boko da rashin hanya da zasu iya fita ko shiga garin a cikin dadin rai.
Garin na Shimfida ya fuskanci Harin 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane wanda ya sabbaba gudun hijira ga mazauna kauyen kimanin watanni biyar koma fiye wanda daga bisani aka samu tsaro inda mutanen garin suka koma gidajensu bisa rakiya da kulawar jami'an tsaro.
Saidai tun bayan komawar mutanen a garin, sun tarar da 'Yan bindiga sun Kona Makarantun Firamare da na Sakandare, Asibiti Makarantun su na koyon Addini duk sun rushe, sana gadar shiga da fita garin da Gwamnati ta fara ginawa domin samun saukin zirga-zirga itama aikin ya tsaya an gaza idawa.
Bugu da kari al'ummar garin sun koka game da halin kunci da suke ciki, kasantuwar ba su iya shiga ko fita daga garin don nemo wasu kayan masarufi, abinci ko magunguna, ko kuma rashin lafiya ta fidda mutum zuwa wata Asibitin face sau daya a mako.
Sun bayyana cewa duk mako guda sau daya ne Ranar Lahadi Sojoji ke masu Rakiyar fita da komawa garin, sunce a baya sau biyu ne a sati amma kasantuwar Jami'an tsaron da ke masu rakiya sun ce, kudin man da karamar hukumar Jibiya ke basu don yin wannan Rakiya (Escot) basu isar su, don haka saidai su gama da hakuri.
"Hakan na nufin ko wace irin lalura ta rashin lafiya garemu da mata masu haihuwa da sauransu saidai mu rungumi kaddara" inji wani mazaunin garin da muke zantawa da shi.
Duba da wannan yanayi da Al'ummar Shimfida suke ciki mun tuntubi shugaban Karamar hukumar Jibiya, Alhaji Sabi'u Maitan wanda ya sheda mana cewa, Tabbas duk halin da garin Shimfida yake ciki, sun sani, amma Al'amari ne da yafi karfin karamar hukuma. Aikin Jiha ne, kuma Aiki ne yayi wa Gwamnati yawa, amma tana sane da halin da suke ciki, kuma tana bin abin daki-daki, yace tabbas za'azo kansu."
Yace "Gwamnatin jihar Katsina bata manta da Al'ummar Shimfida ba, bata manta da irin kokarin su na zabar Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Radda ba, yace duk da halin da suke ciki a lokacin zabe sun kadawa Gwamna Radda Kuru'un su, yace tabbas Gwamna yasan haka kuma za'azo kansu.
Game da zancen bada tallafi ga jami'an tsaro domin rakiyar mutanen garin na Shimfida, Honorabul Maitan ya bayyana cewa duk wani Tallafi da karamar hukumar ke badawa a baya don taimakawa al'umar wanda ya shafi kudin mai da sauransu Karamar hukumar na badawa babu abinda ta fasa.
www.katsinatimes.com
07043777779, 08036342932