JAM IYYAR PDP A JAHAR KATSINA TA KARA KACAMEWA !!!....
- Katsina City News
- 20 Jan, 2024
- 754
...An zargi mutanen Yakubu lado da Saba alkawali
...hedkwatar PDP ta kasa ta zama "cash and carry"
Muazu Hassan @Katsina Times
Jaridun Katsina Times sun ga wasu takardu da wasu jiga jigan Jam iyyar PDP suka sanya ma hannu, takardun da suka kara tabbatar da munin da rikicin jam iyyar PDP a jahar Katsina tayi.
Takardar farko na wani zama da akayi a Kano a gidan Dakta Mustafa inuwa dake jam bulo Wanda masu ruwa da tsaki na jam iyyar suka hadu suka cimma matsayoyi takwas.
Matsayar da itace zata warware matsalar jam iyyar da kuma sanya ta cigaba .daga cikin matsayar akwai 1 jam iyyar zata ci gaba da aiki da Kwamitin riko da uwar jam iyyar ta kasa ta kafa 2 warware matsalar zabbabbun yan Kwamitin riko na kananan hukumomi.3 fadada Kwamitin masu da tsaki na jam iyyar 4 asusun hada kudin karo karo daga duk mai hali a jam iyyar, don tafiyar da jam iyyar.5 kafa Kwamitin bada shawara don tafiyar da jam iyyar 6 haduwa a Kaduna don kara jaddada abin da aka tattauna a Kano.7 Rubuta takardar "query " ga jafaru Runka.
A takardun da Katsina Times ta samu duk masu ruwa da tsaki da suka halarci wannan zama sun amince sun kuma sanya ma takardar hannu.
Mutanen da suka rattaba hannu sune 1, senator Umar tsauri 2 senator Yakubu lado 3 senator Ahmad Babba kaita 4 Dr Mustafa inuwa 5 Dr Garba Matazu 6 Hon sirajo Makera 7 Hon lawal Danbaci.
Takardu na biyu da jaridun suka gani, ta takardar bayan taron na "meeting"da akayi a Kaduna ranar 17 ga watan Disamba 2023. Wanda masu ruwa da tsaki Goma sha biyu suka halarta.cikin su har da dakta Mustafa inuwa da Yakubu lado,Mutane 8 suka bada hakuri. Wadanda ba a gayyato ba amma suka halarta su 7 dukkanin yaran sanata Yakubu lado ne.
A zaman aka karanta matsayar da aka cimmawa a zaman Kano, kuma zaman ya amince da a tura ma uwar jam iyya cewa wannan shine matsayar duk masu fada aji na Katsina akan jam iyyar PDP ta ci gaba.
Wannan "minutes of the meeting" ya samu sanya hannun shugaban Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam iyyar da kuma sakataren sa, sune sanator Umar tsauri da lawal Rufai safana.
Kwatsam duk da wannan yarjejeniya da amincewa sai ga tsohon shugaban jam iyyar da aka nada a Kano lawal Dambaci Wanda kowa ya San cewa yaron sanata Yakubu lado Dan Marke ne,ya kai jam iyyar kara a babbar kotun Katsina.a ranar 29 ga watan Disamba 2023
Anyi zaman kotun farko da sanya ranar sauraren karar,a ranar 18 ga watan janairu 2024 sai kuma a ranar 12 janairu 2024 sai ga babbar hedkwatar PDP ta kasa ta sake nada sabon Kwamitin riko na jaha Wanda ta sallami nada ba tare da tuntunbar masu ruwa da tsaki na jam iyyar PDP na Katsina ba.
Daga cikin wadanda aka nada akwai wadanda ko mazabarsu ba Wanda zai iya kawo wa a siyasance.
Wannan ya sanya.jiga jigan jam iyyar guda uku Dr Mustafa Inuwa , sanata Umar tsauri da Sanata Ahmad Babba kaita a wasikar suka jawo hankalin shugaban jam iyyar na kasa ( Na riko) zaman da suka yi a Kano da Kaduna da kuma matsayar da suka cimmawa, suka jaddada cewa wannan matsayar sun sanar ma da uwar jam iyya a rubuce, amma duk da haka sai ga uwar jam iyya ta Saba abin da aka tsaya akai.
Sannan suka ce, jam iyyar PDP a Katsina da masu ruwa da tsakin cikin ta basu amince da duk wata matsaya da ga uwar jam iyyar da ta Saba ma wancan ba.
Sannan suka hada duk sakamakon zaman da akayi a baya suka aika ma uwar jam iyyar, suka kuma aika ma duk wani mai fada aji na cikin jam iyyar a Najeriya.
Wani jigon PDP a bangaren sanata Yakubu lado ya tabbatar ma da jaridun Katsina Times cewa suna son kwace PDP daga abin da ya Kira tsaffin cima zaune kuma kuraye.ya kara da cewa muna son Cusa masu damuwa da bakin cikin da sai sun bar jam iyyar.
Yayin da dayan Bangaren ke jin tsoron cewa, barin jam iyyar ga bangaren su Yakubu lado suyi yadda suke so da ita.zai zama wani tsohon Dan takarar gwamna a jam iyyar zai ma yar da jam iyyar kayan jarin sa ne na samun kudin shiga .
Dukkanin Bangarorin biyu sun tabbatar ma da jaridun Katsina Times cewa hedkwatar jam iyyar ta kasa ta zama " cash and carry" da kudin ka sai abin da ka ke so za ayi maka. Hatta kalmomin da za ayi amfani dasu a takardar da kake bukata sai yadda ka zaba.
Ma aikatan da shugabannin jam iyyar PDP na kasa ana zargin sun zama iya kudin ka iya kidan da za a kada maka.
Katsina Times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
07043777779 08057777762