TARIHIN MARIGAYI MALAM MUHAMMADU ABDULBAQI KATSINA

top-news


@ Katsina Times 
An haifi Alhaji Makkiyu a Unguwar Yan shuni dake cikin binnin Katsina a 1937 Yafara karatun Alkur'ani a wajan mahaifiyar sa Inda ya sauke Alkur'ani yana Dan shekara 9 yafara karatun tauhidi a wajen mahaifiyar sa sannan yaci gaba da karatun ilimin Addini a wajen Mahaifinsa Malan Abdulbaki wanda mashahuri ne wajan ilmi Addini da kuma rubutu Wanda yayi rubuce rubuce masu yawa Harma a ingila dakin karatu da Al'adu dakwai irin rubuce rubucen sa shi mahaifin Alh Makkiyu, Malan Makkiyu ya karanta fannonin Ilimi da dama Kamar : Alkur'ani, da Hadisi, da nahawu, da fiqihu, da lugga.

 Daga cikin Malaman sa da kwai : Mahaifiyarsa Hajiya Maimuna, wadda aka fi sani da "HAJIYA MALAMA" sai mahaifinsa Malam Abdulbaki " MALAM ABBA" sai Malam Ala Tsohuwar kasuwa, sai Malan Falalu Darma, sai Malan Hamisu na Galadanci, da Malan Attahiru U/Alkali, sai kuma yayan sa Liman Malan Abbate,
 Daga cikin daliban da ya karanatar da kwai :
 Dalibar sa ta farko Hajiya Rakiya Diyar Waziri zayyana,  da Hajiya Iyani yayar Su Mai Girma chi garin Katsina, Wanda har gida yake zuwa suyi karatun sai Sarkin Katsina Alh Muhammadu Kabir Usman, sai Sallaman Katsina Alh Umme yar Aduwa, sai Alh Lawal Kaita, sai Malan Abba Aliyu, da Malan  Alhasan s/Unguwa, da Malan Abubakar Bilbis, da sauran su da dama inda har yanzu Haka Yana koyar da Mai Martaba Sarkin Katsina na yanzu Alh Dr Abdulmumin Kabir Usman duk a ranakun Litinin da Laraba da Kuma Juma'a 

 yafara koyar da karatu tun yana Dan shekara 9 a gidan Wazirin Katsina wato Waziri Zayyana, A labarin da muka samu a wajan Hajiya Rakiya Diyar Waziri zayyana Kuma Mata ga Mai Martaba Sarkin katsina tace"Wata Rana lokacin tana yarinya bazata wuce shekara Bakwai ba sai taga Mallam Makkiyu zai gitta ta Kofar gidan su Yana dauke da littattafai ( A lokacin babu injin na buka littafi sai dai a rubuta da hannu a saida to Mahaifiyar shi Marubuciya ce tana rubuta littatafai Yana saida Mata kamar su Tauhidi Ahalari Ishiriniya da wuturiya da sauransu) sai naje nacema mahaifiyata wadda daiyace ga Sarkin Katsina Muhammadu Dikko Ina so lallai sai ta sayamani tace to in kirawo shi na kirashi a lokacin shima Yana Yaro sai mahaifiyata tace mashi zan sayamata Tauhidi tunda dama dashi ne ake fara Karatu Amma Ina so karika zowa kana koyamata Dan na aminta da natsuwar ka sai yace to zankoma gida in nemi izini tukun da yake mu bamayin komai sai da izinin iyayanmu da yakoma gida aka bashi izini yazo yafada Mata shikenan aka Kama karatu har takai ga bama ita kadai ba hadda sauran matan cikin gida da yake gidan Waziri Babban gidane Kuma sabo da tsarin mutanan da Maza basa shiga rannan Malam yazo zai shiga sai ya iske Mai gida zaune a Kan kujera cikin Zaure(Wato Waziri Zayyana) Sai ya duka yagaishe shi sai yace mashi Yaro Ina zaka yace zanje cikin gida wajan Uwar gida Ina koya masu karatu Mai gida yace Kai Dan Ina ne? Malam Yagayamasa daga inda yafito to dayake shi Waziri yasan Mahaifin Mallam sai yace mashi wane irin karatu kake koya masu Mallam yace Ina koya masu Tauhidi yace karantamani inji ai Nan fa malama Yakama karatu Waziri yaji karatu yace lallai wannan ba Yaro bane babbane Kuma naji Dadi yakawo Anini daya yabashi to daganan duk sadda zaije karatu sai Waziri yabayar da sadakar kudi da godia haka suka chi gaba da karatu har akayi ma Hajiya Rakiya Auren fari

Hakanan Kuma sunyi Karatu da Maimartaba Sarkin Katsina Alh Muhammadu Kabir tun lokacin da shi Sarkin Bai Dade da yin auran fari ba sun fara karatunne da wani littafin Fiqihu Mai suna RISALA haka suka chi gaba da karatu harma suna fita wajan gari chan sabon gida hanyar Bugaje inda Malam zayayi ma Sarki Karin karatu shikuma Sarki sai koma karkashin inuwar tsamiya yaci gaba qwamawa har sai ya hardace bayan Rana tayi sanyi Kuma sai koma gida

 wata Rana suna zaune suna wannan karatu sai ga Sarkin Katsina Usman Nagogo Mahaifin Sarki Kabir sai wuce suka tashi sukayi gaisuwa yace mi kuke a Nan sukace karatu muke yace wane irin karatu sukace Karatun Fiqihu ne Sarki yaji Dadi yayi masu Addu'a ya wuce haka dai karatu yacigaba da tafiya har lokacin da aka nada Muhammad Kabir Sarautar Magajin Garin Katsina Sai suka cigaba da yin karatu a gidan Magaji Wanda suna farawa bayan isha'i har sukai karfe 11 Na dare daga Nan sai suci abinci ayi bankwana

 Lokacin da Allah yatabbatar ma Sarkin Katsina Kabir Sarauta sai sukayi shawara sabo da aiki yayi mashi yawa suka Mai da Karatun ranakun Lahadi da Alhamis da yamma haka ake har Allah yadauki rayuwar Sarki inda Kuma suka dasa Karatun da Dansa Sarkin Katsina Alh Abdulmumin Kabir Usman Wanda da farko kullun ake Karatun bayan anyi Sallah Magriba sai ayi karatu idan angama karaatu ayi Sallah isha'i to lokaci na tafiya jikin Mallam na Kara yin rauni sai aka maida karatu Ranakun Litinin da Laraba da Kuma Juma'a

Mallam Makkiyu ya halarci wasu kasashe Kamar Saudi Arabia da Ingila da Jamus Misira da Kuma makwabatanmu Nigar da Kuma Cotonou

Hakanan Kuma Mallam Manomi ne kasancewar  a wancan lokaci babu abinda akafi Maida hankali a kansa kamar Nima wannan Dalilin ne yasa shima Mallam yake Noma sosai Wanda Bayan angama noma Kuma sai a dawo a zauna Makaranta a cigaba da chin abinda aka noma yayi Noma Masara Kasar bakoro lokacin Amininsa Makaman Katsina Tukur shine yakarfafa Masa guyiwa wajan noman Kuma yabashi wata katuwar gona musamman Dan yin Wannan noman yazama duk Alhamis Malam Yana zuwa gonarsa ta Bakori wani lokaci yakwana daya zuwa biyu Kuma yadawo hakanan Kuma yayi noman Dankali a Garin Wagini cikin kasar Batsari sannan Kuma da kwai wata Katafariyar gona Wanda Sarkin Katsina Alh Muhammadu Kabir Usman yabasu aro suna nomawa shi da Sallaman Katsina Alh Umme Yaradua inda daga baya yamallakama su ita

 yafara karatun Tafsir na Azumi tun yana da shekara 20 daga cikin Abokan sa da suka taso tare da kwai Marigayi Alkalin Alkalai Malan Aminu Ibrahim, sai Alh Sada Yusifa,  sai tsohon shugaban kotun daukaka kara ta Kasa Umar Abdullahi, sai Malan Bature Darma, sai Alh Ali Mai Chanji, Sai Alh Lawal na Alkali, da Alh Ibrahim Masta Al Baba, sai sen. Abu Ibrahim da yahaya Ibrahim

 dakuma mnyan Aminan sa:
 marigayi mai martaba sarkin Katsina Alh. Dr. Muhammadu Kabir Usman, da mai martaba sarkin binnin gwari Malam Zubairu da mai martaba marigayi sarkin Dass Alh. Bilyaminu da maigirma sarkin sudan Alh.Shehu malami, da Iyan Katsina Aminu, da Sallaman Katsina Alh Umme Yar Adua, wazirin Shariffan Katsina Abba Yahaya, Alh Iro Isansi, Alh Idi Labari, Sarkin Shariffai Abba Hamza, 

 yanzu yana da mata 3 yaya 24 jikoki 115 kuma yana cikin koyar da karatu yanzu haka a cikin rayu a yanzu Yana da shekara 85 a rayuwa Allah yakara ma rayuwa Albarka Allah yaja da rai yakara lfy

 SANARWA TA MUSAMMAN.
Wannan rubutun ba wakilan Katsina Times suka rubuta shi ba.mun dauko shi a shafin Facebook na Hussaini k yar adua..bamu da cikakken suna ko adireshin marubucin.
Munyi amfani da rubutun don girmamawa ga Marigayin Allah ya jikan shi.

NNPC Advert