Gwamnan jihar Katsina ya biya Bashin Miliyan 12 na Ma'aikatan Masafkan Baƙi Katsina Motel

top-news

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya biya Bashin Miliyan 12 na Ma'aikatan Masaukan Baƙi

Zaharddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya Tallafawa Hukumar Masaukan Baƙi na Katsina Motel da Naira Miliyan 12 don biyan bashin ma'aikata na tsawon watanni hudu da suka gada.

Bashin ya taru ne a sanadiyar raunin jagoranci daga wadanda sabbin shugabannin suka gada kamar yanda Shugaban Hotel din Katsina Motel na Katsina, Isah Alhassan ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin.

Yace "A lokacin da muka zo wannan gida mun iske komai ya tsaya, ma'aikata babu albashi, babu Kwastomomi balle mu iya biyan albashi har mu ajewa gwamnati wani abu" 

"A ka ida dama Dukkanin Masaukan Bakin mu, mu ke wa kammu albashi muke biyan wuta da ruwa da duk wasu hakkoki hadda harajin gwamnati, to amma sakamakon rashi kula sai Motel din ya zama babu hatta albashin da zamu iya biya, amma da taimakon Allah, da dafawar Kwamishinan ciniki da masana'antu da Masaukan bakin suke karkashin sa, muka samu muka farfaɗo da masaukan bakin, a cikin 'yan watannin da muka zo muka ci-gaba da biyan albashi, hatta dan abinda ya samu na haraji muka cigaba da biyan gwamnati, ganin haka yasa maigirma Gwamnan jihar Katsina ya tallafa mana da kudi kyauta ba bashi ba yace mu biya tsohon bashin da muka gada". inji shi.

Isah ya yaba da godiya ga Gwmnan jihar Katsina Malam Dikko Radda inda yace a madadin ma'aikatansa na nan Katsina fiye da 120 suna kara mika godiya ga Gwmnan jihar Katsina da mataimakansa bisa irin yanda suka fidda ma'aikatan Katsina Motel daga cikin kunci.

Shima a jawabinsa na godiya, Babban Manajan gidajen bakin na jihar Katsina, Hon. Sani Aminu  Dangumau yace, Gwmnan jihar Katsina mutum ne na talakawa kuma talakawa ne a gabansa bashi da wani tunanin da ya wuce su, don haka suna kara mika godiya a madadin dukkanin ma'aikatan na jiha, kuma yace "yanzu haka kowane ma'aikacin mu dake fadin jihar Katsina albashinsa ya shiga hannun sa na wata hudu cur, kuma suna godiya."

A karshe yayi kira ga dukkanin ma'aikatan na jihar Katsina da su cigaba da bada kokarin su na raya gidajen Masaukan bakin kamar yanda aka shedesu da kokarin hakan a baya, yace "Katsina Motel gidansu ce basu da wani wajen samun abin mu'amula na yau da kullum da ya wuce wajen don haka su nuna kishi da kula kamar yanda gwamnatin Katsina ta faranta masu. 

A karshe ya tabbatar wa al'umma jihar ta Katsina cewa akwai manyan gyare-gyare da za ai ma masafkan bakin wanda kowa zai cigaba da san barka.

NNPC Advert