Hukumar Sufuri ta jihar Katsina ta sayi Sabbin Motoci 7 a cikin watanni 7

top-news


Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

A ranar Alhamis ne 28 ga watan Disamba Hukumar Sufuri ta (Katsina State Transport Authority)  KTSTA ta gabatar da Sabbin Motoci kirar Toyota Homer, ga Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda.

Motocin na Sufuri guda bakwai kamar yanda Shugaban Hukumar ta KTSTA Haruna Musa Rigoji ya bayyana, sun samar da su ne bisa umarnin mai girma Gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Umar Radda.

Rigoji ya ce, "Duk da yanayin tsadar mai, a haka muke tattalawa muyi kokari muga mun cika Umarnin Gwamna a lokacin da ya saimana Motoci 40 na Sufuri yace mu yi kokari muga duk wata mun aje kudin da zamu sayi mota ko da guda daya ce. Don haka muke hakuri da duk wasu bukatu don muga mun faranta ran al'ummar jihar Katsina." Inji Rigoji

Tun da farko Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda ya godewa Allah, ya juma jinjinawa Shugaban Hukumar ta KTSTA bisa na mijin kokari da sukai na ganin sun samar da wadannan motoci guda 7 a cikin wata 7. Gwamnan yace wannan abin a yaba ne. Gwamna Radda ya bayyana cewa "shi yasa muka samu masu amana da al'ummar Katsina ne a gabansu. Yace game da samun wadataccen matsuguni kuma yace yanzu haka akwai babban waje da hukumar ta KTSTA zata koma muna nan muna shirin saida tsohon wajen don zuba kudin a sabon wajen don al'umma su yalwatu duba da Motoci sun yi yawa fasinja sunyi yawa wajen kuma ya matse.

A karshe ya godewa al'ummar jihar Katsina bisa gudunmawa da goyon baya da suke bawa gwamnatinsa.

An gabatar da Motocin ne a gidan Gwamnatin jihar Katsina bisa rakiyar Daraktoci da kuma wasu daga Direbobin Hukumar ta KTSTA.