Yadda Emefiele Da Zainab, Tunde, Gambari Da Wasu Gagga Suka Kimshe Kuɗaɗen Najeriya – Mai Binciken CBN.
- Katsina City News
- 23 Dec, 2023
- 763
Mai Binciken Harƙallar Kuɗaɗe a Babban Bankin Najeriya (CBN), Jim Obazee, ya bankaɗo yadda CBN a ƙarƙashin korarren gwamnan bankin, Godwin Emefiele, Zainab Ahmed, Tunde Sabiu, Gambari, suka ɓoye dukiyar da Najeriya ta mallaka a asusun ajiya har sama da Naira Trillion Daya a Najeriya, Amirka, Birtaniya da Chana, ba tare da iznin da sanin tsoho Shugaban kasa Bahari ba
Mai Binciken Musamman, ya kuma gano yadda Emefiele shi da wa’anasu a Gwabnatin Bahari su ka saci biliyoyin nairori da Dalalulin Amurka tare da haɗin bakin wasu jami’an Gwabnati
“Kuma Emefiele sun cire Dala miliyan 6.23, kwatankwacin Naira biliyan 2.9, a kan Naira 461 kowace dala ɗaya.
Obazee ya bayyana haka a cikin rahoton da ya gabatar, tare da bayar da shawarar a gurfanar da Emefiele, Zainab Tunde da wasu mutun 14 a kotu, kuma a ɗaure su, tare da wasu manyan jami’an CBN su 23, cikin su kuwa har da mataimakan gwamnan CBN, saboda sun karya doka.
A Birtaniya kaɗai, Mai Binciken CBN na Musamman ɗin ya gano cewa Emefiele ya ɓoye Dala miliyan 543.4 a wani asusun ajiya da ba a taɓa cirar kuɗaɗe a cikin sa ba.
A cikin rahoton da ya damƙa wa Shugaba Bola Tinubu a ranar 9 ga Disamba, wanda kwafen rahoton ya biyo ta kan gidajen Jaridu Obazee ya bankaɗo wasu Laifuka da dama waɗanda sai a kotu ne za a nemi Emefiele da sauran du su kare kan su.
A ranar 28 ga Yuli, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Obazee Mai Binciken Musamman kan CBN.
Ya umarce shi da ya kafa gaggan ƙwararrun da suka ƙunshi jami’an yaƙi da rashawa domin ya gudanar da aikin sa yadda za a yi nasarar bankaɗo zargin satar maƙudan kuɗaɗe.
A lokacin naɗin sa, Obazee shi ne Shugaban Majalisar Rahoton Harkokin Najeriya, FRCN tsakanin 2011 zuwa 2017.
Copied Madogara TV/Radio