Kamfanin MAX AIR Ya fara Jigilar Masu Zuwa Umra
- Katsina City News
- 21 Dec, 2023
- 498
Daga Shafin Mobile Media Crew
Kamfanin jiragen Sama na Max Air ya fara aikin jigilar maniyyata masu aiki Umarah na shekara ta 2023/2024.
Daga shafin Mobile Media Crew
A daren ranar Laraba 20/12/2023, shahararen kamfanin jiragen na Max Air, a karkashin hamsha'kin Dan kasuwar nan na jihar katsina, Alh. Dahiru Mangal ya fara aikin jigilar maniyyata masu aikin Umarah na shekarar 2023/2024 a Fillin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
Kamfanin jiragen na Max Air ya saukaka farashin tikitinshi "Tickets" duba da halin da al'umma suka samu kansu a cikin hauhawar farashin kayyaki a Nigeria, Jirgin zai ringa tashi sau biyu a sati.
Fara jigilar , za'a cigaba da gudanar da ita, Tun daga yanzu har zuwa cikin azumin watan Ramadan na shekara mai zuwa ta 2024, wanda anyi haka ne don a saukaka ma al'umma, wanda Allah ya baiwa ikon zuwa domin gudanar da ibada a cikin sauki
Mobile Media Crew ta zanta da wasu daga cikin Maniyyatan da zasu gudanar da ibadojin su, inda suka bayyana fatan alheri su tare da yima Allah godiya, akan yadda kamfanin ya saukaka don samama al'umma sauki.
Alh. Adamu Maina Waziri tsohon ministan Yan sanda Nijeriya ya bayyana yadda ya samu kanshi a cikin jirgin na kamfanin Max Air tare da bayyana fatan Alheri shi ga yadda kamfanin ya yi tunani na fara irin wannan aikin alheri.
Jirgin na Max Air mai kirar 777 dauke da maniyyatan kusan sama da mutane 400 ya tashi a Laraba a filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa na Malam Aminu Kano dake jihar kano da misalin karfe 11:00 na dare zuwa Jiddah.