ShopRite zai rufe harkokinsa a Kano a 2024 kimanin shekara guda da bude reshe a Kaduna
- Katsina City News
- 17 Dec, 2023
- 1021
Dalilin Da ShopRite Zai Bar Kano
Katafaren kamfanin kasuwanci na ShopRite ya sanar da shirinta na rufe harkokinsa a Jihar Kano daga shekarar 2024 mai kamawa.
ShopRite, wanda ya shekara tara yana gudanar da harkokinsa a katafariyar kasuwar zamani ta Ado Bayero Mall ya ce zai bar Kano ne saboda gasa da rashin samun ciniki yadda suke so.
Hukumar gudanarwar Ado Bayero Mall ta bayyana rashin jin dadinta da ficewar ShopRite, ind ta kara da mika goron gayyata ga sabbin masu zuba jari da za su maye gurbin ShopRite a kasuwar a 2024.
Ficewar ta ShopRite daga Kano na zuwa ne bayan takwaransa, Games ya tattara kayansa ya fice daga Ado Bayero Mall.
Sanarwar da Daraktan Ado Bayero Mall, Ike Okeke ya fitar ta ruwaito ShopRite na bayyana matsin tattalin arzikin Najeriya a matsayin dalilin da za su bar Kano.
Rahotanni sun nuna a cikin makon nan ne hukumar gudanarwar kamfanin da ke kula da ShopRite ya aike wa ma’aikatansa takardar shirin ficewarsa daga Kano.
Sai dai kanfanin ya ce zai ci gaba da harkoki a wasu jihohi, har ya shawarci ma’aikatan su jaraba neman aiki a sauran sassan nasa.
Kimanin shekara guda ke nan da ShopRite suka bude reshe a Jihar Kaduna, makwabciyar Kano.
A 2014 ne ShopRite suka fara zuwa Kano, cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya da a makwabtaka.
Sai dai ana ganin sun yi fama da gasa sosai daga sauran manyan katafarun shaguna da suka rika fadawa da inganta harkokinsu da kuma hulda da abokan ciniki.