Yadda Al’adu Nagari Ke Rainon Sinawa
- Katsina City News
- 27 Aug, 2023
- 775
Babbar Ganuwa Dake Jiayuguan Tana Taimakawa Ga Yayata Kyawawan Dabi’un Al’ummar Kasar Sin Jiayuguan, wuri ne dake yammacin lardin Gansu na kasar Sin, inda a ranar 20 ga watan Agustar shekara ta 2019, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar gani-da-ido, don kara fahimtar ayyukan kiyaye babbar ganuwar kasar mai dogon tarihi. Shugaba Xi ya jaddada cewa, da zarar an ambaci sunan kasar Sin, abin da mutum zai tuna ita ce babbar ganuwar kasar. A kan kuma tuna ta a duk lokacin da aka ambaci al’adun gargajiyar kasar Sin. Babbar ganuwar kasar Sin, da Koging Yangtze, da Rawayen Kogi, muhimman alamomi ne na al’ummun kasar, wadanda ke shaida nagartattun dabi’un mutanen kasar.
Jiayuguan, shi ne mafarin babbar ganuwar kasar Sin daga yammaci a lokacin daular Ming. A yayin rangadin da ya kai wajen, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya dace a gudanar da ayyukan raya al’adun dake tattare da babbar ganuwa da kara gadon su, da ci gaba da tallata nagartattun dabi’un al’ummar kasar Sin. Kuma a ‘yan shekarun nan, lardin Gansu na kara daukar matakai don bincike game da muhimman darajojin al’adun babbar ganuwa, da inganta ayyukan bayyana al’adun, tare kuma da kiyayewa gami da gudanar da ayyukan kirkire-kirkire a kansu.
A halin yanzu, tsawon babbar ganuwa dake yankin Jiayuguan, ya zarce kilomita 43. A watan Agustan shekara ta 2019, shugaba Xi Jinping ya hau ganuwar dake wajen, inda ya ganewa idanunsa yadda aka tsara wajen, ya kuma jaddada cewa, babbar ganuwar kasar Sin na dauke da kyawawan dabi’un al’ummar kasar Sin, wato yin kokari ba tare da kasala ba, da zama tsintsiya madaurinki daya ba tare da yin kasa a gwiwa ba, tare kuma da nuna kishin kasa, abun da kawo yanzu ta riga ta zama muhimmiyar alama ta al’ummar kasar Sin gami da al’adunsu
Yanzu haka, mutane suna bin sahun shugaba Xi na ziyartar babbar ganuwa dake yankin Jiayuguan, inda suke hawa matakala suna hangen tsawon ganuwar daga nesa, don kara fahimtar yadda babbar ganuwa ta ratsa manyan duwatsu, da sanin dogon tarihin dake tattare da ita.
He Shuangquan, manazarci ne dake aiki a cibiyar nazarin kayan tarihi dake lardin Gansu na kasar Sin, ya bayyana cewa: “Garin Jiayuguan gami da babbar ganuwar dake bayansa, ba ayyukan soja ne kawai ba, har ma suna kunshe da tarihin sama da shekaru 100, wadanda ke bayyana dabi’un al’umma. Wato sun nuna babban karfin al’ummar kasar Sin wajen kirkiro manyan abubuwa masu ban al’ajabi.”
A wurin, an gina wani dakin adana kayan tarihi mai suna dakin adana kayan tarihi na babbar ganuwa ta Jiayuguan, dake zama irinsa na farko da ya nuna kayan tarihin dake kunshe da al’adun babbar ganuwa a kasar Sin. An gina shi ne bisa siffar babbar ganuwa, inda aka rataya wani babban zane mai fadin murabba’in mita 220, da ake kira “Babbar Ganuwa Mai Tsawo”, wanda ya bayyana kyan muhallin babbar ganuwa dake bangarorin gabas, da tsakiya, gami da yammacin kasar Sin. Haka kuma an baje kayan tarihi masu daraja sama da 2200 a ciki, wadanda ke bayyana dogon tarihin dake tattare da babbar ganuwar kasar, da nunawa al’umma yadda aka yi kokarin gina ta. Kamar yadda daya daga cikin masu ziyartar dakin ya ce, ya kara fahimtar dogon tarihi game da babbar ganuwar kasar Sin, da nagartattun dabi’un al’ummar kasar Sin, kuma yana alfahari da ganinsu.
Kiyaye babbar ganuwar kasar Sin, ba zai rasa nasaba da kokarin da ake yi na kiyaye kayan tarihin da aka gada daga kaka da kakanni ba, sa’annan ana kokarin yi musu kirkire-kirkire. A ranar 2 ga watan Yunin shekarar da muke ciki, shugaba Xi Jinping ya halarci taron karawa juna sani kan gado gami da raya al’adu a Beijing, inda ya jaddada cewa, ya kamata a dauki sabon nauyi a fannin raya al’adu, da takaita wasu sabbin ra’ayoyi da tunani da shawarwari da suka shafi al’adu da aka fitar, bayan da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kira babban taronta karo na 18. Xi ya kuma ce, ya dace a himmatu wajen kiyaye al’adun gargajiya da kayan tarihin da muka gada daga kaka da kakanninmu, kamar yadda muke kokarin kare rayukanmu, domin kara tallata al’adun gargajiyar kasar Sin.
makoma mai haske.
A wurin yawon shakatawa dake garin Jiayuguan, ana gabatar da wani kasaitaccen wasan kwaikwayon gargajiya mai taken babbar ganuwa, wanda shi ne irinsa na farko da ya bayyana al’adun babbar ganuwa da labaran da suka shafi jarumai masu kare al’ummar kasar Sin daga harin kasashen waje, ko wadanda suka bayar da babbar gudummawa wajen shimfida “hanyar siliki” a tarihin kasar Sin, ciki har da Zhang Qian, da Huo Qubing, da Xuan Zang da sauransu, al’amarun da suka burge masu kallo kwarai da gaske.
A ‘yan shekarun nan, a tsohon garin Jiayuguan, ana kokarin hada wasu al’adu tare, ciki har da na babbar ganuwa, da na kan iyaka, da na hanyar siliki, don sanya sabbin abubuwa a cikin al’adun babbar ganuwa, da raya sana’ar yawon bude ido yadda ya kamata.
A wajen taron karawa juna sani kan gado gami da raya al’adu da aka yi a ranar 2 ga watan Yunin shekarar da muke ciki a Beijing, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, al’adun kasar Sin na da hakuri sosai, wato suna kunshe da mabambantan abubuwa da yawa, al’amarin da ya kafa alkiblar musanyar al’ummun kasa, da aza tubali ga kasancewar addinai daban-daban a kasar.
Al’adun kasar Sin na da dogon tarihi, wadanda suka samu karfi da kuzari daga dabi’un al’ummar kasar, wato neman zama tsintsiya madaurinki daya. Kara musanya da yin koyi da juna, ya kara sanya sabbin abubuwa gami da wadatar da al’adun kasar Sin. Don haka, ya dace a ci gaba da tsayawa kan adalci, da yin koyi da musanyar ra’ayi tsakanin juna, da yin hakuri da juna, da kiyaye alamomin al’ummun kasar yadda ya kamata, da ci gaba da gadon al’adun gargajiya, ta yadda al’ummun kasar Sin za su samu bunkasa a duk fadin duniya.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin al’adu da yawon shakatawa ta birnin Jiayuguan, Zhang Xun, ya bayyana cewa, Jiayuguan zai ci gaba da kiyaye al’adun da suka shafi babbar ganuwa, da kara koyon hikimomi daga al’adun gargajiya da aka gada zuriya bayan zuriya, da kuma sabuntawa gami da yin kirkire-kirkire ga al’adun gargajiya, a kokarin fadakar da al’umma game da tushe da muhimmancin al’adu. (Murtala Zhang)