Kungiyar Ushaqun Nabiyyi (S.A.W) ta Nada Aminu Mamman Dee Sarkin Yakin Sharifai Garkuwan Masoya Annabi.
- Katsina City News
- 11 Dec, 2023
- 644
Katsina Times
A ranar Lahadi 10 ga watan Disamba Shahararriyar Kungiyar Sharifai ta Ƙasa Ushaqun Nabiyyi (S) Maso Yabon Annabi (S) da Hausa karkashin jagorancin Sharif Auwalu Sadiq da Sarkin Sharifain Najeriya suka tabbatar masa da ita.
Katsina Times ta zanta da Alh. Aminu Mamman Dee da ya samu wannan babbar Karramawa inda ya nuna farin cikin sa da wannan matsayi, yace "Na ga girman sunan, yau gashi ance Nine Sarkin Yakin Iyalan Annabi (S) kuma garkuwa Masoya Manzon Allah, hakika wannan kyakkyawan sheda ce da zanyi alfahari da ita, ina godiya kwarai da gaske." Inji shi.
Shugaban na Ushaqu Nabiyyi ta Kasa ba bayyana sakonsa kai tsaye ga Daukacin Al'ummar Musulmi musamman Masu Yabon Annabi (S) da cewa kowa ya tsarkake niyyarsa yayi abinsa don Allah a kuma cigaba da hidima ga shugaba Muhammad Rasulullah (S) kamar yanda Alh. Aminu Mamman Dee yake wanda har ya jawo masa wannan matsayi da muke fata Allah da manzonsa suyi sheda akan wannan matsayi Duniya da Lahira.
Yace "kuma ma Alhamdilllah wannan matsayi da Alh. Aminu ya samu ko nace sheda gashi har wasu kungiyoyi suma sunga dacewar sa akan suma su girmama shi da nasu shedar irin su jama'atul shu'ara,il Islam karkashin jagorancin Malam Surajo da shugaban Lajana da shugaban Irshadu." Yace wannan abin alfahari ne.
Taron da ya gudana a dakin taro na ERC dake Ƙofar sairi ya samu halartar manyan baki shehinnai da Sha'irai maza da mata daga yankunan Gombe, Kano, Kaduna, Zamfara, Bauchi, Sokoto, da sauransu.