Sojoji Sun Hallaka Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Mai Suna Yellow Jambros Da Yaran Shi A Dajin Shiroro Cikin Jihar Neja.
- Katsina City News
- 10 Dec, 2023
- 725
Sojoji Sun Hallaka Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Mai Suna Yellow Jambros Da Yaran Shi A Dajin Shiroro Cikin Jihar Neja.
Rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch ta kai wani hari ta sama a ranar Laraba, 6 ga watan Disamba, 2023, a ƙaramar hukumar Shiroro jihar Neja, inda ta kashe ƴan ta’adda da dama ciki hadda fitaccen ɗan ta’adda da masu garkuwa da mutane, Yellow Jambros.
Ƴan ta’addar sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke yunƙurin tsallakawa kogin Jikudna a gundumar Galadima Kogo, inda suka nufi Wurukuvhi a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Kafin harin, ana bin sawun Yellow Jambros tare da tawagarsa daga jihar Zamfara zuwa jihar Neja a kan babura 13 a iyakar jihar Kaduna da Neja, inda suka nufi ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
A Kusasu wasu ƴan ta’adda 5 da ke kan babura sun shiga cikin ayarin tawagar Yellow Jambros, inda adadin baburan ya kai 18, inda suka nufi gaɓar kogin Jikudna.
A bakin kogin, ƴan ta’addar da babura 18 sun shiga wani katon ƙwale ƙwale a ƙoƙarin su na tsallakawa tare da cudanya da sauran ƴan ta’adda a faɗin kogin. A wannan lokacin ne aka ba da izinin gudanar da farmakin. Farmakin dai ya yi tasiri yayin da ya kashe Yellow Jambros da takwarorinsa, ya lalata baburansu tare da nutsar da jirgin ruwan.
Duk da cewa ba a saba ganin yadda ƴan ta’addan ke tafiya cikin ayarin babura 18 da rana tsaka ba, amma bisa ga dukkan alamu Yellow Jambros da ƴan tawagarsa sun ɗauka cewa an dakatar da kai hare-hare ta sama biyo bayan wani abin takaici da ya faru a Tudun Biri da ke Jihar Kaduna, inda suka so su yi amfani da wannan damar.
Yellow Jambros da tawagarsa sun yi garkuwa da mutane da dama a hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma wasu al’ummomi a jihohin Kaduna, Neja, Katsina da Zamfara.
Ko a watan Oktoban 2020, Jambros wanda akafi sani da suna Mohammed Sani, an zarge shi kisan Mutane sama da Hamsin a jihar Zamfara saboda rashin samun kuɗin fansa.