KWAMANDOJIN YAKIN GAZZAH SH. YAHYA AS-SINWAR SHUGABAN KASAR GAZZAH Haihuwarsa da karatunsa.

top-news


Daga shiek Aminu Aliyu Gusau

Sh. Yahya Ibrahim Hassan As-Sinwar an haife shi ne a shekarar 1962 a cikin sansanin 'yan gudun hijira da ke gari Khan Yunis a Gazzah. Iyayen shi suna cikin wadanda yahudawa suka kora daga gidajensu da ke birnin Askalan a nakba (Musiba) ta 1948. 

(Falasdinawa suna kiran musibar da ta samesu a shekarar 1948, lokacin da yahudawa, tare da izini da taimakawar turawan Biritaniya, suka kore mafi yawansu daga garuruwansu da gidajensu suka mamaye mafi yawan kasar Falasdin, suka shelanta kafa kasar Isra'ila da "Nakba". A lokacin Falasdinawa sun tarwatse - wasu suka koma Gazzah da zama, lokacin tana karkashin Masar, wasu kuma suka koma West Bank a lokacin tana karkashin Jordan . Da yawa kuma sun rarrabu a cikin kasashen duniya.)

Shine (iyayen na Yahya Sinwar)suka yi gudun hijira zuwa Gazzah, a lokacin tana karkashin Masar.

Yahya Sinwar ya yi karatunshi na faramare da sakandare a birnin na Khan Yunis, daga nan ya wuce Jami'ar musulunci da ke birnin Gazzah inda ya karancin addinin musulunci da harshen larabci. Daga nan ya shiga cikin sahun 'yan gwagwarmaya karkashin Hamas. Yana daya daga cikin wadanda suka kafa bangaren soja na Hamas, watau "kata'ibul Kassam".

Gwagwarmayar shi da yahudawa ta jawo mashi a 1982 aka tsareshi, tsarewar farko a rayuwarshi. Haka ma a 1985 an sake tsareshi. 

A 1989 aka sake kamashi da hanu a cikin kashe yahudawa biyu da Falasdinawa biyu masu yiwa yahudawa infoma. Sakamakon haka ne aka yanke mashi hukuncin daurin rai da rai sau hudu.

A shekarar 2011 kamar yadda muka ambata a baya an saki Yahya Sinwar daga kurkuku bayan ya shafe shekaru 22 a ciki. Sakin nashi ya biyo bayan wata musaya da aka kai karshenta tsakanin Hamas da Isra'ila - Hamas za su saki wani sojan Isra'ila mai suna Gilad Shalit wanda ya shafe shekaru biyar a hunnunsu, su kuma Isra'ila za su saki Falasdinawa 1,026 daga cikin Falasdinawan da suke tsare da su a cikin gidajen yarinsu.

Zamu kammala in sha Allah.

Modibbon Gusau.
1/12/23.
Mun ciro daga shafin Attajadid Media na Facebook