ASALIN MALAMAN ƁATAGARAWA
- Katsina City News
- 04 Dec, 2023
- 1017
Daga Kasim Batagarawa
Malaman Ɓatagarawa su ma sanannu ne kamar yadda mahukuntan garin suke, watau malamai ne waɗanda Hukuma ta mallaka masu sha'anin Jama'a wajen harkokin addinin Musulunci.
Su ke jagoranci a cikin al'amurran rayuwar jama'a, kamar limancin Garin Ɓatagarawa da ɗaurin aure da zanen suna da tafsiri, da ba da fatawa da shawara da sauran harkokin addinin musulunci irin su karantar da jama'a karatun Allo da litattafai. Sun kasance masu Zuhudu da kuma taka-tsantsan wajen raɓar shuwagabanni.
Zuhudun ya haɗa har da gudun yin mu'amala da masarautu muddin ba masarautun suka neme su ba don ba da wata fatawa ko warware wasu matsalolin addini ko harshen Larabci.
Wannan ya nuna su ba Malaman Fada ba ne.
Iyaka suna yin hidimar Limanci ne don cancanta da kuma sauke nauyin da Allah ya aza masu. Sun kasance baya ga hidimar addini, sun riƙe kiwo da noma da Kwarami a Matsayin sana'a.
A fannin kiwo, ya ƙunshi kiwon dabbobi kamar su Shanu, da Awaki da Tumaki, don haka kuma suna saida mai da nonon shanu da na Awaki.
Suna ba da magungunan ciwace-ciwacen Shanu iri-iri kamar bauru da ƙurajen fatar shanu. Bayan wadatar da kansu da nama, suna saida wa Runzawan Ɓatagarawa wadannan dabobi don samun kuɗin shiga. Har wayau suna kiwon kaji da Zabbi da Agwagi da Tantabaru.
Sun shahara wajen ba da naƙul-ƙula da magungunan ciwace-ciwace da ke damun mutane, misali kamar maganin ciwon hali da ciwon da ya shafi jiki. Ciwon hali kamar su sata, hauka da sauran halayen da al'umma ke ƙyama.
A fannin noman tsire-tsire da itace kuma sukan noma Gero da Dawa da Masara da Wake da Kuriga da Gyaɗa da Dankali da Rogo da Taba da Tasshi da Tattasai da Gauta da Tumatur da Kyarma da Yakuwa da Zogala da Lalle da Mangwaro da Dorowa da Rama da Kabushi da Duma da Kwarya da Auduga da Kubewa domin ci da sayarwa.
Bugu da ƙari sun ba da gudummuwa wajen tattalin arzikin Ɓatagarawa wajen saƙa tufafi don sayarwa da kuma sutura.
JERIN LIMAMAN ƁATAGARAWA TUN KAFIN ZUWAN TURAWA ZUWA YAU DA KUMA SHEKARUN DA SUKA YI LIMANCI
1. Abdulmumini (Nini) ɗan Ummaru Kaki
2. Yusuf Ɗan doton tsafe
3. Muhammadu Datti ɗan Ummaru Kaki
4. Abdullahi Ɗan mage ɗan Sada ɗan Nasiru ɗan Ummaru Khaki
5. Liman Halliru Makki ɗan Muhammadu Datti ɗan Ummaru Kaki ? - 1965
6. Liman Mu'azu ɗan Ummaru Uba ɗan Abdulmumini nini ɗan Ummaru
Kaki-1965 - 1975
7. Liman Abubakar Ɗan Aye ɗan Mamman Ƙyanƙyari ɗan Muhammadu
Datti ɗan Ummaru Kaki -1975 - 1991
8. Liman Abdulkadir ɗan Abubakar ɗan Muhammadu Giɗaɗo ɗan
Abdulmumini Nini ɗan Ummaru Kaki -- 1991- 2005
9. Liman Usman Imam Ɗan Halliru Makki ɗan Muhammadu Datti ɗan
Ummaru Kaki - -l-2005 - 2008
10. Liman Maiwada ɗan Mu'azu ɗan Ummaru Uba ɗan Abdulmumini Nini
ɗan Ummaru Kaki-2008 - zuwa yau.
Fulani ni ne da suka samo asali ne daga Malle ko Malli (kasar Mali). A Karni na (15) ne kamar yadda masana Tarihi suka kawo cewa, Mallawa ko Wangarawan da suka taso daga wani yanki da ake tsammanin na Senegambia Region ne a shekarar (835AH) (1431/32) (Tijjani, 1997), suka yi tafiyar shekara talatin da ɗaya (31) zuwa Kano, ƙarkashin jagoransu Abdurrahman Zaite Babban Malami mai tsoron Allah. Sun iso ƙasar Hausa a ƙarni na 15 kan hanyarsu ta zuwa Makka. Sun sauka garuruwa da yawa cikin ƙasar Hausa don yaɗa Addinin musulunci.
Mallawa sun fara sauka a Gobir, wasu suka wuto Katsina, suka kafa cibiyar yada addinin musulunci a Kwami, sannan suka wuce Kano. (Yahaya Sauri 1998).
Ahmadu da matarsa Hau'wau ne suka fara zama a Kwami, inda ya fara koyar da karatu. Malam Ahmadu yana da Almajirai da yawa, tun daga waɗanda suka zauna Kwami zuwa waɗanda ke zuwa daga ƙasar Katsina da kewaye ɗaukar karatu.
Ɗan Ahmadu na farko ana kiransa Muhammadu wanda ya gaji Mahaifinsa sosai wajen Ilimin Addini.Bayan Ahmadu ya samu jika mai suna Ummaru Kaki, sai Allah ya yi masa rasuwa a farko-farkon ƙarni na 16.
Allah sarki, ashe Ummaru Kaki jikan Ahmadu shi Allah ya nufa da zai haifi ƴaƴa da yawa har zuriyar KWAMI ta yaɗu. Inda ya haifi diya biyar Muhammadu Datti, Abdullahi Abba, Abdulmumimi Nini, Nasir da Usman Mani.
A cikin ƙarnin na (18) Wani Malam ma Malam Usman Bakaduba daga Mali ya zaɓi ya zauna a Kwami, kasantuwarta cibiyar koyon Addinin Musulunci. Ya haifi ɗa mai suna Muhammadu Na Alhaji. Da ya tashi tafiya Makka sai ya bar ɗansa Muhammadu Na Alhaji hannun Malam Ummaru Kaki Inda ya samu tarbiyya da ilimin addinin Musulunci.
Ana kyautata zaton cewa Muhammadu Na Alhaji ya bar Kwami yana da shekaru sha takwas (18). A shekarar (1770) ya tafi Sokoto wajen Shehu Ɗanfodiyo don cigaba da neman ilimi. Ya dawo Kwami lokacin yana da shekaru Arba'in (40). Ya zama babban malami daga nan sai ya koma Runka.
Malam Ahmadu ya sa ma wurin da ya sauka Kwami.Dalilin da ya kira wurin Kwami, shi ne lokacin da Ahmadu ya sauka a Kwami, Sarkin Katsina na wannan lokaci ya ba shi shugabancin wurin da kuma abin da ke kewaye da shi, amma bai karɓa ba.
A cikin dalilan da ya sa bai karɓi Sarauta ba, ya ce ''ni kam ina da KOMI a hannuna,'' watau ilimi da dukiya, don haka ba ya bukatar sarauta. To wannan kalma ‘komi’ ta sa ake kiran wurin da ya zauna, Kwami.
Duk da bai anshi shugabanci ba, ba a yin komi sai an shawarce shi. Farfesa Dankoussau 1970 ya bayyana ma'anar Kwami da 'komi banza'. Dalilin faɗin haka kuwa shi ne duk lokacin da
Ummarun Dallaje ke buƙatar wani abu na sayarwa, sai a ce mashi a tafi 'Komi banza' can za a samo shi da arha. Haka ma Kamaradden Imam da Dahiru Kumasi 1995 sun fassara 'Kwami' da wadatar komi.
Daga baya ma, Muƙaddashin Sarkin Katsina na Ɓatagarawa ya ankara da bunƙasar da Kwami take yi na tara Jama'a, sai ya ji tsoron kada gaba Kwami ta danne Ɓatagarawa. Sai ya yi wa mutanen Kwami tayin mulki, kuma su dawo Ɓatagarawa da zama, amma sai suka ƙi amintuwa da haka. Magana ta kai wajen Sarkin Katsina, a inda Sarki ya ce su koma Ɓatagarawa da zama a ba su limancin garin.
Suka koma gida suka yi shawara. A nan ne Muhammadu Datti ɗan Ummaru Kaki ya yarda ya koma Ƙofar Arewa, Ɓatagarawa.
A lokacin da Turawa suka raba ƙasar Ɓatagarawa da ta Dutsinma, an ba Ɓatagarawa Sarautar Hakimci a shekarar (1923). Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya buƙaci Kwamawa da su yi Hakimcin Ɓatagarawa, amma sai suka buƙaci cigaba da limanci. Aka ɗauko Malam Ibrahim Jamo daga Makurda aka ba shi sarautar Ɓatagarawa a matsayin Hakimi wanda hakan ya sa ya zama Hakimin Ɓatagarawa na farko.
(Shi Malam Ibrahim Jamo jinin Malam Muhammadu Gigama ne, yana cikin tawagar Wangarawa ko Mallawa da suka iso Ƙasar Katsina. Malam Ahmad ya sauka a Kwami sai shi Malam Muhammad Gigama ya matsa ya sauka a Maƙurɗi duk a Ƙasar Batagarawa nan ya yi rayuwarsa har ya rasu, kabarinsa na nan a Makurɗi. Yakan je Abukur ba da karatu ya dawo Maƙurɗi ya kwana. Zuriyarsa sun taso sun dawo Unguwar Alkali kuma ana ce masu Bani Hambali cikin Birnin Katsina).
Bayan bayyanar Shehu Ɗan Fodiyo, Kwamawa sun nuna amintuwa da ba da goyon baya ga Jihadinsa. Duk da irin matsin da Sarkin Katsina na wancan lokacin yake wa magoya bayan Shehu Danfodiyo, amma su Kwamawa ba su samu wannan matsin ba, saboda bai taɓa musguna wa mutanen Kwami ba dangane da irin goyon baya da suke ba Jihadin Shehun ba.
Kwami ta zama sansanin Mayakan Na'Alhaji wato Zorawa lokacin da ake shirin kwace birnin Katsina daga hannun sarakunan Habe.
( Zorawa su ma Fulani ne waɗanda suka zauna a Kwami kuma suka ba da gudunmuwa wajen Jihadin Shehu Ɗan fodiyo a Ƙasar Katsina.
Su ne mayaƙan da Muhammadu Na Alhaji ya yi Jihadi da su wajen ƙwace birnin Katsina. Malam Jibir abokin Muhammadu Na Alhaji shi ne Jagoran Zorawa, sun kasance wancan lokacin in sun gama daukar karatun wajen maluman Kwamawa sai su tafi kiwo Dajin Zori. A lokacin suka tarar da kufan Barawa, suka raya shi Ƙarƙashin jagorancin Usman Ƙosau. Sarkin Katsina Ibrahim ne ya maido Zorawa lokacin su Abdullahi Iya Nadabo Ƙofar Ƴandaka. Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya yi masu sarauta a garuruwa irin su Bakori da Ƙankara da Ƙetare da Ɗanja da Tsiga.)
Bayan korar Sarakunan Haɓe daga sarauta a duk yankin Ƙasar Katsina. Ita ma Ƙasar Ɓatagarawa ba ta tsira ba, Fulani sun kore wadanda ke mulkinta, inda Ɓatagarawa da Kwami suka kasance cikin mulkin Muhammadu Dikko ɗan Muhammadu Na Alhaji
Lokacin da saɓani ya tsananta tsakanin Su Ummarun Dallaje da Ummarun Dunya da Muhammadu Dikko, sai Muhammad Dikko ya baro Katsina ya dawo Kwami da zama ta zama fadar mulki. Sai a shekarar (1844) Ƴandaka Hassan Dan Muhammadu Dikko ya koma Tsauri da zama.
Amintuwar da Sarakunan Katsina da na Ɓatagarawa suka yi wa Kwamawa ya sa suka ta yi masu tayin sarauta, domin ba da tasu gudummuwar wajen jagorancin Al'umma. An samu Kwamawa daga baya sun riƙi sarautu kamar haka
1. A lokacin Mallamawa Murtala aka fara samun mai unguwar Kwami na farko, Malam Abubakar Maigatari. Bayan rasuwarsa, ɗansa Malam Badamasi ya gaji sarautar. Bayan rasuwar Malam Badamasi a ranar 3/4/1993, Mallamawa Bara'u ya nemi ba da sarautar ga Malam Ahmadu dan Badamasi amma Allah bai nufa ba, shi ya sa har yanzu babu mai unguwar Kwami. yanzu Kwami ta zama wata unguwa a garin Ɓatagarawa, ƙarƙashin kulawar mai unguwar Tsauni.
2. Wakilin maganin Sarkin Katsina Alhaji Abubakar Ibrahim Wanda Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumimi Kabir Usman ya nada.
3.. Galadiman Gotomawa (ƳarMakera) Gotomawa Ƙauye ne cikin yankin gundumar Rawayau ta Ƙaramar Hukumar Kurfi cikin Jihar Katsina.Lokacin da Sarautar Rawayau da ta Gotomawa suka faɗi, sai Sarkin Katsina Sir. Usman Nagogo ya buƙaci amininsa Alhaji Abubakar Ƙudus da ya bi Malam Buhari (wanda ƙane ne ga Sarki Muhammadu Dikko) su tafi ya raka shi Rawayau don su yi mulkin Rawayau da Gotomawa. Abubakar Ƙudus ya faɗa wa Mai Martaba Sarki cewa, ai shi ba mai zama ba ne, sai dai ƙanensa Muhammadu Madani ya bi shi. Muhammadu Madani ya raka malam Buhari Rawayau don yin mulki, shi kuma Muhammadu Madani ya yi mulkin Gotomawa a Matsayin Galadima, har zuwa shekarar 1962 lokacin da Allah Ya amshi ransa. Ya bar 'ya'ya hudu, Dahiru da Rakiya da Muntari da Zinatu.
Bayan rasuwarsa mutane dabandaban sun riƙe sarautar Galadiman Gotomawa har sai a shekarar 2016 ta dawo hannun Dahiru Muhammad Madani.A zamanin Rawayau Buhari Allah ya albarkace shi da ɗiya ɗaya mai suna Amina, wadda bayan rasuwar Rawayau Buhari a cikin shekara ta dubu da daya da dari tara da sittin da shidda 1966, mijinta Wakili Haruna ya gaji sarautar Rawayau.
4.. SARAUTAR ƊAN-MASANIN ƁATAGARAWA
Kasantuwar Kwamawa mutane ne masu ilimin Addinin Musulunci, hakan ya sa Masarautar Ɓatagarawa ƙarƙashin Mallamawa Dikko a shekarar 2001 ta naɗa ɗaya daga cikin Kwamawa mai suna Khadi Abdulƙadir Abubakar Ƙudus a matsayin Ɗan Masanin Ɓatagarawa na farko. Ya yi sarautar har zuwa shekarar da ya rasu 2010. Ya bar 'ya'ya hudu, AbdulRashid da Hikma da Laila da Muhammadu Datti.
Kwamawa sun gina Masallatan farko-farko a Ɓatagarawa don sallar Jam'i. Sun gina rijiyoyi a dukkan kusurwowin Ɓatagarawa huɗu wato gabas da yamma da arewa da kuma kudu.
Daga cikin su akwai sananniyar rijiyar da ake kira rijiyar Uwar 'ƴaƴa a kudancin Ɓatagarawa. Dalilin da ya sa ake ce mata uwar-ƴaƴa shi ne a zamanin da rijiyar take ganiyarta, akwai wadanda suka yi imanin cewa duk matar da ake tsammanin ba ta haihuwa ko kuma ta daɗe ba ta haifu ba, idan ta sha ruwan rijiyar za ta haifu.
Mata da yawa da ke cikin garin Ɓatagarawa da kewaye sukan zo su sha ruwan wasu kuma a diba a kai masu don su samu haifuwa. Akwai kuma wata sananniyar rijiya da ake kira rafin-waje daga arewacin Ɓatagarawa. Gina waɗannan rijiyoyi sai ya zamar masu sadakatil jariya ga jama'ar yankin.
Sarakunan Katsina sukan nemi malaman Kwami wajen roƙon Allah idan wata fitina ta shigo gari ko aka ji labarin za a kawo yaƙi, kuma cikin ikon Allah sai a samu nasarar abin da aka roƙa wajen Allah.
Allah ya tsare Kwami da mutanenta daga yaƙe-yaƙen da aka yi da kuma harin kamen Bayi. Ba a taɓa shiga Kwami ba don yaƙarta ko don kamen Bayi.
Kwami yanki ne kamar kilomita ɗaya (1) Arewa-maso-Yamma da garin Ɓatagarawa. A yau ta hada da yankin Rubu da Tsauni da Agama da Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Katsina (FCE) da Rukunin gidaje masu saukin kuɗi (low cost) na Ɓatagarawa da Kwalejin kimiyya da fasaha ta Jihar Katsina (Hassan Usman Katsina Polytechnic).
A halin yanzu, mafi yawan zuri'ar Kwamawa suna nan zaune a Kofar Arewa Batagarawa, Rubu,Ƴargigo, Babban Duhu, Bakiyawa, Maidabino, Dabaibayawa, Kuraye, Danmusa, Kuka Sheka, Garwa, Gunki ta kasar Rimi. Dutsinma, KankaraKatsina, Kano, Lagos, Maiduguri, Gombe.
Akwai wasu kuma a Ƙasar Chadi da Misra da kuma Sudan sanadiyar zuwa aikin Hajji da kuma neman Ilimi suka bar Zuri'a a Ƙasashen.