Wanene AIG Yahaya S. Abubakar Shugaban Rundunar 'Yansandan Shiyya Ta 14 Kaduna da Katsina...?
- Katsina City News
- 30 Nov, 2023
- 597
Katsina Times
AIG Yahaya S. Abubakar, mni, ya fara aiki a hukumance a shiyya ta 14, hedkwatar Katsina, wanda ya kunshi rundunar ‘yan sandan jihohin Kaduna da Katsina.
AIG Yahaya S Abubakar wanda Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun, PhD, NPM, ya Turo kuma ya kama ya fara AIG aiki a ranar Laraba, 29 ga Nuwamba, 2023.
Sabon mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sandan da aka turo yana da kwarewa sosai ta fannoni da dama
AIG Yahaya S. Abubakar Wanda ya fito daga garin Uba da ke karamar hukumar Hong a Jihar Adamawa, mamba ne a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru a Kuru ta kasa, kuma ya yi Digiri na biyu. Degree (LLB. Hons) a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.
Aikin sa ya fara ne a watan Mayun 1992 lokacin da ya shiga aikin ‘yan sandan Najeriya a matsayin mamba na Cadet ASP Course 17.
AIG Yahaya S. Abubakar ya gudanar da muhimman ayyuka kamar Asst. Sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar (FCID Annex, Alagbon Close, Ikoyi-Lagos), hedikwatar AIG shiyya ta 15, Maiduguri, da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Yobe.
Ya yi aiki a Tawagar kiyaye zaman lafiya ta kasa da kasa guda biyu, inda ya ba da gudummawa ga tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Laberiya (UNMIL) da kuma wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka a Somaliya (AMISOM) a matsayin babban mai ba da shawara ga 'yan sandan kasar Somaliya.
AIG Yahaya S. Abubakar memba ne a kungiyoyi daban-daban da suka hada da National Institute for Policy and Strategic Studies (mni), Chartered Institute of Public Administration of Nigeria (FCIPAN), Institute of Management Consultant of Nigeria (FIMCN), kuma yana rike da lakabi na Mashawarcin Gudanarwa (CMC). Gagarumar hidimar da ya yi ya ba shi damar samun kyaututtuka da yabo da yawa a cikin gida da kuma na waje.
A cikin wata sanarwa, sabon AIG yana karfafa gwiwar jama’a da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da su hada kai da rundunar ‘yan sandan Najeriya wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a shiyyar.
Ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin hukumomi domin magance matsalolin tsaro da ta addabi a jihohin Kaduna da Katsina.
AIG Yahaya S. Abubakar ya tabbatar wa jama’a cewa duk wani bayani da ya shafi aikata laifuka za a yi amfani da su da cikakken sirri don kare majiyoyin.