Ayyukan raya ƙasa: Gwamnatin Kano ta zata gudanar da wasu muhimman Ayyuka a cikin Birnin

top-news

Gwamnan Kano ya bayyana a shafinsa na Facebook, Katsina City News ta ciro:

Bugu da ƙari cikin zaman da majalisar zartarwa ta gudanar a jiya laraba karkashin jagorancina, majalisar zartarwa ta amince da abubuwa kamar haka:

1- Mun saki kuɗi kimanin miliyan ɗari 8 da 54 (854m) domin fara gudanar da bikin auren zawarawa a jihar Kano.

2- Na naɗa kwamiti na musamman da duba yadda zamu biya dukkanin ƴan fansho dake jihar Kano haƙƙoƙin su.

3- Za'a gyara gadojin sama guda uku waƴanda suke taimakawa ɗalibai wajen shiga makarantun su a bakin ƙofar shiga tsohuwar jami'ar Bayero dake nan Kano, da kuma wacce take a bakin ƙofar shiga Kwalejin koyon ilimi addini ta Malam Aminu Kano hadi da gadar da ke ƙofar shiga makarantar koyon ilimi mai zurfi ta Sa'adatu Rimi. -AKY