Hukumar KAROTA a Kano ta Cafke masu hada haɗa takardar ɗaukar kaya ta boge

top-news

Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta jihar Kano KAROTA ta sami nasarar cafke mutane uku da suke buga takarda ɗaukar kaya ta Waybill.

Hukumar ta ce mutanan da take zargi da buga Waybill ɗin an jima ana nemansu, sai a wannan rana aka samu nasarar cafke su

Hukumar ta dade tana zargin su da wannan mummunan ta'adar wanda hakan har ya sa aka ƙara sabunta Waybill ɗin tare da ƙara masa matakan tsaro 

Daga cikin waɗanda Hukumar ta sami nasarar cafke wa sun hada da; Abdulhadi Iliyasu da Shamsu Rabi'u da kuma Samual Ajaye

Bayan da aka cafke su sun bayyana cewa sun ɗauki sahihiyar takarda guda ɗaya ta hukumar sun kai wa wani mai suna Samuel Ajaye a cikin Sabon Gari domin ya buga musu

Bayan da Hukumar ta cafke Samual Ajaye ya tabbatar mata da cewa su suka saka shi ya buga musu Waybill din har sun bayar da kafin-alƙalami na Naira Dubu ɗari da Talatin

Bayan kammala bincike hukumar ta miƙa su hannun jami'an Yansanda domin faɗaɗa bincike tare da gurfanar da su gaban kotu