KATSINA CITY NEWS TA KOMA KATSINA TIMES
- Super Admin
- 13 Aug, 2023
- 555
Muna farin ciki sanar da cewar daga ranar 15 ga watan Agusta, 2023 zamu canza sunan jaridar 'Katsina City News' zuwa 'Katsina Times'. Wannan matakin ya biyo bayan shawarar da muka yanke domin jaridar ta zama ta kasa da kasa kuma ingantaciyya. Amma dukkan ayyukanmu na baya, suna nan a 'Katsina City News' dinsu kuma za a iya samun su a sabon shafin mu na www.katsinatimes.com.
Kasashe kimanin ishirin da tara ke da manya jaridu a kasar su kuma duk suna amfani da wannan take na 'Times'. Misali,
Khaleej Times a kasar Qatar da
Tehran Times a kasar Iran da
Istanbul Times a kasar Turkey da Pakistan Times a kasar Pakistan da New York Times a kasar Amurka da Japanese Times a kasar Japan da
Hindustan Times a kasar India da Daily Times a kasar Najeriya da Premium Times a kasar Najeriya da Katsina Times a kasar Najeriya.
Mun dakatar da buga jaridar 'The Links News' domin karfafa wa 'Katsina Times' karfi.
Mun tattauna da editocin wasu jaridun na times wadanda zamu rika daukar labaran su, su kuma zasu rika ji daga wajen 'Katsina Times' a duk wani labari daga Najeria da ma yammacin Afrika.
Wannan sabuwar jaridar zata fito da tsare-tsare na ilmantarwa, fadakarwa da kuma zaburarwa a cikin harsunan Hausa da Turanci.
Mujalar 'Katsina City News' mai kawo maku tarihi da hotunan su, zata canza ita ma zuwa 'Katsina Times'.
Muna da dimbin takardun tarihi da hotuna da hukuncin kotuna na zamanin Turawan mulkin mallaka masu cike da tarihi wanda zamu rika kawo maku.
Tarihi na da dandano guda biyu; zaki da kuma daci, saboda haka, dole wani lokaci sai an yi hakuri da abinda muka saki kamar yadda muka same shi.
Zamu yi bikin kaddamar da sabon sunan nan gaba kadan insha Allahu.
Muna neman addu'o'inku da goyon bayan da shawarari da kuma gyara a duk inda aka ga kuskure, domin gyara kayan ka, bai taba zama sauke mu raba ba.
Mun gode.
Allah ya saka da alheri.
Muhammad Danjuma,
Mawallafin jaridun katsina times da jaridar taskar labarai.
08057777762.08020570059