Tarihin Unguwar Al'kali a cikin Birnin Katsina
- Katsina City News
- 21 Oct, 2023
- 1439
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 21,10,2023
Unguwar Alkali
Unguwar Alkali tana nan yammancin gidan waya na Katsina, bangaren Wakilin Kudu. Daga kudu ta yi iyaka da Albaba, ta yamma ta yi iyaka da Darma ta gabas ta yi iyaka da Yansiliyu daga Arewa ta yi iyaka da Unguwar Yarima. Kamar yadda Gambo Ibrahim da Ahmadu Mai Gari suka ce "An kafa Unguwar Alkali a shekarar 1809.
Wanda ya kafata shi ne Alkali Abubakar Dankanda jikan Muhammadu Shumo. Shumo kalmar fillanci ce wadda take nufin wanda aka haifa a cikin watan azumi. Shi Muhammadu Shumo babban Malami ne wanda ya yi kaura daga Futo Jallon, wadda a yanzu take cikin Kasar Senegal, Zuwa Sifawa cikin Kasar Sakkwato. Daga nan ya taso zuwa Makurdi a shekara ta l1750. Wannan Kauye na Makurdi yana nan bisa babbar hanyar Kano zuwa Katsina kusa da Dandagoro. A yanzu ana yi wa wannan Kauye na Makurdi lakabi da suna "Unguwar Liman".
A wannan wuri ne Muhammadu Shumo ya kafa makaranta domin karantar da ilimin addinin Musulunci". Bayan rasuwar Muhammadu Shumo, sai babban dansa mai suna Abu Muhamman ya ci gaba da tafiyar da makarantar kamar yadda mahaifinsa ya yi. Da Abu Muhamman ya rasu sai dansa mai suna Muhammadu Gigamna wanda ake kira da suna "Zakin Makurdi" ya gaje shi. Tarihi Ya nuna cewa a lokacin da Shehu Danfodio ya kaddamar da jahadi a Kasar Hausa, sai ya umurci Sarkin Katsina, Ummarun Dallaje ya aika masa Muhammadu Shumo. Amma da aka bincika sai aka tarras ya rasu. Sai aka tafi da jikansa Zakin Makurdi.
Bayan da Shehu ya gam su da iliminsa, sai ya nada shi Alkalin Katsina. Gambo Ibrahim da Ahmadu Mai Gari sun ci gaba da bayani cewa: "Bayan rasuwar Muhammadu Gigama, sai aka nada dansa Malam Abubakar Dankanda a matsayin AIkalin Katsina. Malam Abubakar Dankanda mutum ne mai đinbin ilimi. Ya shahara kwarai a harkar alkalanci. Wasu bayanai sun nuna cewa wata rana ya tafi ya ziyarci Shehu Usman Danfodio tare da dan wansa Alkali Ahmadu Hambali. Da suka isa, Shehu ya yi masu kyakkyawar maraba ya ce "Yau ga Bako mai Ilimi, iliminsa da ruwa ne, da ya ci Sakkwato, kuma da hazo ne, da ba wanda zai ga wani a Sakkwato. Bayanan sun nuna cewa lokacin da aka nada shi Alkalin Katsina, Malam Abubakar Dankanda ya cigaba da zama a Makurdi daga inda ya ke zuwa Katsina domin Alkalanci. Da ganin haka, sai mutane suka fara guna-guni da tsogwamin cewa ai ya kamata ya tare a Katsina. Babu dalilin da zai sa ya zauna a Kauye ya dinga zuwa Katsina kullum domin gudanar da Shari'a. Sabili da haka ya taso daga Makurdi ya dawo cikin garin Katsina ya kafa Unguwar AIkali. A cikin azure na biyu a gidan, akwai dakalin da AIkali Abubakar ankanda yake zama ya yi shari'a.
A tarihance, Unguwar Alkali, unguwa ce ta Alkalai kamar yadda Gambo Ibralhim da Ahmadu Ibrahim Maigari suka tsara sunayen Alkalan cikin garin Katsina daga 1809-
1968 a cikin littafinsu mai suna Zuru'ar AIkali Ahmadu Hambali da Danginsu" shafi na hudu kamar haka:-
1.AIkalin Katsina Abubakar TDankanda -1809-1842
2. AIkalin Katsina Ahmadu Hambali -1842-1894
3. AIkalin Katsina Usman Majid -1894-1896
4. AIkalin Katsina Aliyu (Alu) -1896-1901
5. AIkalin Katsina Dalhatu -1901-1916
6. AIkalin Katsina Almu -916-1926
7. Alkalin Katsina Ibrahim (Na Kaita) -1926-1949
8. AIkalin Katsina Muhammadu Bello -1949-1954
9. AIkalin Katsina Ibrahim (Maude) -1954-1960
10. AIkalin Katsina Muhammadu Wada -1960-1964
11. AIkalin Katsina Muhammadu Sada -1964-1968
Baya ga wadannan Alkalan da aka jera a sama,
Unguwar Alkali ta samar da wasu mashahuran Alkalai wadanda suka hada da Marigayi Girandi Khadi Alhaji Muhammadu Dodo da Marigayi Girandi Khadi Aminu Ibrahim da Girandi Khadi Isah Muhammadu Dodo. Bugu da kari, akwai Marigayi Alhaji Usman Balarabe da Marigayi
Alkali Mustapha, da Alkali Yusuf Babba da Tsofon Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Tarayyar Najeriya, Mai Shari'a Umaru Abdullahi da sauransu.
Baya ga alkalai masu ilmi, akwai kuma Malamai wadanda suka shahara a Unguwar AIkali. Daga cikinsu akwai Malam Rabi'u ubansu Marigayi Liman Malam Abdu da Liman Malam Mamman limamin masallacin Unguwar
Yarima. Shi wannan Malami ya shahara kwarai ta fannin ilimin AIkur'ani. Sai Malam Bawa mahafinsu Malam idi.
Shi kuma ya shahara a fannin Ramli (watau lissafi da bincike). Akwai kuma shahararren Malamin nan mai suna Malam Sharu mahaifinsu marigayi Malam Ahmadu da Malam Bala da Malam Ali wanda shahararsa ta a kai har Kasashen Nijar, Chadi, Ghana, Tunisiya da Morocco. Shi ya yi ficce ne wajen warkar da mutanen da aljannu suka taba. Wasu bayanai sun nuna cewa shi ne ya kawo wa Marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko wani littafin ilimi da ake kira da suna "Mudawwana" Daga cikin kayan tarihi da ke a unguwar Alkali akwai wani AIkur'ani rubutun hannu wanda ya fi shekara dari. Wannan Alkur'ani yana nan hannun zuri'ar marigayí Alkalin AIkalan Jihar Katsina Alhaji Muhammadu Dodo.
Baya ga wannan akwai Gidan Waya na Katsina wanda aka gina zamanin Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko. Akwai kuma tafkin farar kasa, wanda ake dibar farar kasa domin shafen gidaje a cikin birnin Katsin da kewaye.
Mun ciro wannan Tarihi daga Littafin Tarihin Unguwannin Birnin Katsina da kewaye na hukumar Adana Kayan Tarihi da kyautata Al'adu ta jihar Katsina ta buga