Bayyanar hoton Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali da Jan Hijabi ya tayar da Kura
- Super Admin
- 04 Aug, 2023
- 807
Tun bayan zagayawar da wasu hotuna na marubuciyar a social media da ta dora da wasu jama’a na raka Sabon kwamishina na ma’aikatar Addinai ta jihar Kano Shehu Tijjani Sani Auwalu Wanda dan jam’iyyar NNPP ne ita kuma Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ‘yar Jam’iyyar APC wadda ta yi shura a cikinta Wanda ba ta Boye akidarta ya janyo ce-ce ku-ce Wanda ya janyo har sai da marubuciyar ta Kara jaddada shahadarta na cewa ita halastacciyar’yar jam’iyya ce ta APC kuma Tana nan Daram ba inda ta je. Da Wakilinmu ya tattauna da ita kan ko dai ana zawarcinta ne a jam’iyyar NNPP? Bayan doguwar Dariya marubuciyar ta ce “ siyasa daban mu’amala daban don haka ita tana nan a jam’iyyar APC amma kuma hakan ba zai hana ta mu’amala da Wadansu kebantattun mutane da suke wata jam’iyyar ba. Misali biyayya ga Ali Niass wajibi ce Shehu Tijjani Shehina ne biyayyarsa umarni ce don haka sabanin jam’iyya ba zai shiga wannan mu’amalar ba. Sannan Shugaban Karota makwancina ne dan’uwana ne ka ga wannan ma ba alaka ce ta siyasa ba. Da sauran mutane da dama Wanda alakar da ke tsakaninmu ta fi ta siyasa. Sannan ni marubuciya ce alkalamina na iya aiki kan kowa ko dai don fadar alheri ko kuma don gyara in har na takaita kaina kan siyasa wannan shi ma kuskure ne don na riga zama marubuciya da siyasa. Don haka ina nan a jam’iyyar APC Wadanda ba su ji dadi ba suna tunanin Santsi ya debe ni su yi hakuri Ina nan a tabo”