Tsohon Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari zai jagoranci Kwamitin sulhu na Gwamnan Ondo da Mataimakin sa

top-news

Ganduje shine ya kafa kwamitin sulhun na gwamnan jihar Ondo da mataimakinsa domin warware rikicin da ke tsakaninsu .
 
 Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa kwamitin sasantawa da za a yi sulhu tsakanin Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo da mataimakin sa, Lucky Aiyedatiwa, da nufin kawo karshe, rashin fahimta.
 
Taron ya gudana ne a ranar Juma’a 6/10/2023 a hedikwatar jam’iyyar APC ta kasa Abuja.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Tsohon Gwamnan jihar Katsina, Rt. Hon.  Aminu Bello Masari da Lawal Abbas Garba a matsayin sakataren kwamitin.
 
Sauran mambobin kwamitin sun hada da M.A Abubakar, Tsohon Gwamnan jihar Bauchi, Adegboyega Oyetalo, Tsohon Gwamnan Osun, Obafemi Hamzat, mataimakin gwamnan jihar Legas, Martin Elechi, Tsohon Gwamnan jihar Ebonyi, Sanata Jack Tyale, Sanata Florence Ita Giwa, da Senator Takunbo Airu.