Yanzu Jam’iyyar APC ta Samu Jagoranci da Saiti a Katsina, — Ahmad Dayyabu Safana.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06032026_132959_FB_IMG_1772803788102.jpg


Daga Auwal Isah Musa.

Mai taimaka wa Shugaban Majalissar Wakilai ta Kasa kan ayyuka na musamman, Honorabul Ahmad Dayyabu Safana, ya bayyana cewar yanzu ne jam’iyyar APC ta samu cikakken jagoranci da tsari a Katsina, bayan kammala zaɓen sabbin shugabanninta na jiha.

Safana ya bayyana hakan ne a wata zantawa ta musamman da jaridun Katsina Times a ranar Juma’a, inda ya yi amanna cewar nasarar da Dr. Bishir Gambo Saulawa ya samu ta zama shugaban jam’iyyar APC na jihar za ta kawo sabon salo da daidaito a tafiyar jam’iyyar.

“Yanzu jam’iyya ta samu jagoranci kuma ta samu saiti. Wannan zaɓe da aka gudanar ya dora komai a kan turba madaidaiciya. Insha Allahu, a cikin tafiyar da za a yi daga yanzu, za a ga abubuwa suna tafiya yadda ya kamata,” in ji Safana.

Ya ƙara da cewar, zuwan Gambo Saulawa kan wannan kujera alama ce ta cewa shugabancin da aka samu yanzu abin yarda ne kuma amintacce, yana mai tabbatar da cewar zai jagoranci jam’iyyar cikin tsari da zai kawo ci gaba ga jam’iyya da al’ummar jihar Katsina baki ɗaya.

Safana ya kuma yaba da rawar da gwamnan jihar, Dikko Umar Radda, ya taka wajen samar da yanayi mai kyau da haɗin kai da ya bai wa kowa, inda kowa ya samu cikakkiyar damar bayyana ra’ayinsa yayin gudanar da zaɓen shugabannin jam’iyyar.

A cewarsa, tsarin shugabancin gwamnan wanda ke bai wa kowa dama, ya taimaka matuƙa wajen tabbatar da cewar an gudanar da zaɓen cikin lumana, fahimta da haɗin kai.

“Duk abubuwan da aka aiwatar a zaɓen nan an yi su ne da ra’ayin jama’a. Ba wai wani mutum guda ya zauna ya tsara komai ya yi yadda yake so ba,” in ji shi.

Ya jaddada cewar duk wani abu da aka gudanar bisa ra’ayin jama’a yana samun karɓuwa cikin sauƙi, kuma al’umma za su tashi tsaye su kare irin wannan tsari domin sun san cewa an yi shi ne bisa amincewarsu.

“Idan al’umma suka san cewa an yi abubuwa da ra’ayinsu, za su ba da gudummawa ga ci gaban jam’iyyar cikin farin ciki. Tsakani da Allah, zuwa yanzu ina ganin komai ya tafi yadda ya kamata kuma babu wata matsala,” in ji Safana.

Follow Us