EMEKA UMEAGBALASI: ZARGIN ƘARYAR DA AMURKA TA DOGARA DA SHI HAR TA KAI GA BARAZANAR KAI WA NIJERIYA HARI

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28012026_170301_IMG-20260128-WA0149.jpg

Rahoto daga jaridar New York Times

@Katsina Times

Jaridar New York Times, ɗaya daga cikin manyan jaridun duniya da ke Amurka, ta gudanar da bincike mai zurfi kan asalin bayanan da ƙasar Amurka ke dogaro da su wajen iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Nijeriya.

Binciken jaridar ya gano cewa wani ɗan ƙabilar Ibo ne mai suna Emeka Umeagbalasi, wanda ke da shagon sayar da kayan gyaran motoci a kasuwar Onitsha, shi ne ke wallafa bayanan ƙanzon kuregen da ake ta yaɗawa, waɗanda Amurka ke amfani da su a matsayin hujjojinta.

Jaridar ta gano cewa Emeka a wani ɗan ƙaramin shagonsa mai ɗauke ɗaya da yake gudanar da harkokin kasuwancinsa tare da ƙaramar kwamfutarsa (laptop) a gabansa, wadda yake amfani da ita wajen rubuce-rubuce da wallafa bayanai a yanar gizo.

New York Times ta ce Emeka yana da wata ƙungiya mai suna International Society for Civil Liberties and Rule of Law, wadda ya kafa tare da matarsa Blessing tun shekarar 2008, kuma suke tafiyar da ayyukanta gaba ɗaya ta yanar gizo.

Jaridar ta bayyana cewa ta hanyar wannan ƙungiya ne Emeka ke rubuce-rubucensa da yaɗa su a kafafen sadarwa na zamani.

Rahoton ya ƙara da cewa duk hujjojin da jami’an gwamnatin Amurka (har da Shugaban Ƙasa) ke dogaro da su, sun samo asali ne daga rubuce-rubucen da Emeka ya wallafa a shafin ƙungiyarsa.

New York Times ta tambayi Emeka ko ya taɓa ziyartar wuraren da yake iƙirarin ana kai wa Kiristoci hare-hare da kisan kiyashi. Sai ya amsa da cewa a’a, yana dogaro ne kawai da rahotannin da yake gani a yanar gizo.

Ya ƙara da cewa kullum yana bibiyar bayanan da ake wallafawa, sannan yana amfani da Google Map domin tantance wuraren da ake ambata.

Emeka ya tabbatar da cewa bai taɓa wuce jihohin yankinsu ba a tafiye-tafiyensa.

Dangane da karatunsa kuwa, Emeka ya ce bayan kammala Sakandare bai samu damar zuwa makarantar gaba ba. Sai daga ya shiga buɗaɗɗiyar Jami’a (National Open University).

Emeka ya bayyana wa New York Times cewa ƙididdiga da bayanan da ya wallafa kan kisan Kiristoci a Nijeriya sune ake amfani da su a Amurka, inda ya ce yana jin farin ciki da alfahari da hakan.

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu yana aiki kan wani sabon rahoto da ya shafi halin da Kiristoci ke ciki a Nijeriya, musamman dangane da abin da ya kira hare-haren masu tsattsauran ra’ayi ko kuma masu iƙirarin jihadi.

Jaridar New York Times ta yi ƙoƙarin jin ta bakin fadar Shugaban Ƙasar Amurka dangane da binciken da ta gudanar, amma haƙar su ba ta cimma ruwa ba. 

Haka kuma, jaridar ta nemi jin ra’ayin wasu ’yan majalisar Amurka da suka fi zaƙewa a wannan batu, ciki har da Sanata Ted Cruz, Sanata Moore da Sanata Smith, sai dai duk ƙoƙarin su bai yi nasara ba.

Follow Us