An Kammala Ganawa Don Daukar Ma’aikatan Lafiya a Ranar Alhamis

Kwamitin Ganawa don ɗaukar ma’aikatan lafiya ya isa Santar Katsina domin kammala zagaye na ƙarshe na aikin ganawar. A halin yanzu,....

Katsina City News December 03, 2025  ·  12:00 AM
| 849 Views


Kwamitin Ganawa don ɗaukar ma’aikatan lafiya ya isa Santar Katsina domin kammala zagaye na ƙarshe na aikin ganawar. 

A halin yanzu, an kammala ganawa a Santoci shidda daga cikin Santoci bakwai da aka ware. Waɗannan Santoci sun haɗa da Funtua, Malumfashi, Dutsinma, Kankia, Mani da Duran, inda aka yi ganawa da masu nema daga Ƙananan Hukumomi 28.

Ganawar da ake gudanarwa a Santar Katsina, wadda take a harabar Hukumar Kula da Lafiyar Farko ta Jiha, za ta ɗauki kwanaki biyu Laraba 3 ga Disamba zuwa Alhamis 4 ga Disamba. Masu neman aikin daga Ƙananan Hukumomin Batsari, Batagarawa, Jibia, Katsina, Kaita da Rimi ne ke halarta. An yi ganawa da masu nema daga Batsari, Batagarawa, Jibia da Rimi a ranar Laraba, yayin da Katsina da Kaita za su yi ganawa a ranar Alhamis.

Za a iya tuna cewa kwamitin ya bayyana tun da farko cewa za a ɗauki mutum 1,200 aiki a tsarin, tare da bai wa ma’aikatan wucin gadi wanda suka jima fifiko.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 8?