EFCC Ta Tsare Tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 189

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11082025_203528_FB_IMG_1754942917541.jpg

KatsinaTimes 

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta tsare tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, bisa zargin cire kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya da suka kai kimanin naira biliyan 189.

Majiyarmu daga EFCC, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa Tambuwal ya isa hedikwatar hukumar a birnin Abuja da misalin ƙarfe 11:30 na safiyar Litinin, inda ake ci gaba da yi masa tambayoyi kan zargin.

Majiyar ta bayyana cewa, waɗannan kuɗaɗe an cire su ne a cikin sabawa Dokar Hana Halatta Kuɗaɗen Haramtacciyar Hanya ta 2022. Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a bayyana lokacin da aka yi wadannan cire-cire ba.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ƙi yin tsokaci kan lamarin.

Tambuwal ya yi mulkin Jihar Sokoto daga 2015 zuwa 2023, kuma kafin haka ya kasance Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya tsakanin 2011 zuwa 2015.

Tun bayan kafuwarta a shekarar 2003, EFCC ta kasance ta gaba-gaba wajen binciken tsofaffin gwamnoni, ministoci, da manyan jami’an gwamnati da ake zargin sun aikata laifukan rashawa da karkatar da kudade.

A 2010, EFCC ta kama tsohon Gwamnan Delta, James Ibori, kafin daga bisani a tura shi Birtaniya inda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 13 saboda halatta kuɗaɗen haramtacciyar hanya.
A 2015, Hukumar ta cafke tsohon Gwamnan Adamawa, Murtala Nyako, bisa zargin karkatar da fiye da naira biliyan 29.
A 2016,  Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido, da ‘ya’yansa, sun fuskanci shari’a kan zargin karkatar da kudaden jihar.
A 2021, EFCC ta kama tsohon Gwamnan Abia, Orji Uzor Kalu, wanda aka yanke wa hukuncin shekaru 12 a gidan yari kan zargin satar naira biliyan 7.1, sai dai daga baya kotu ta soke hukuncin saboda matsalolin tsarin shari’a.
A 2023, An gurfanar da tsohon Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, bisa zargin cin hanci da karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

A mafi yawan lokuta, waɗannan binciken na EFCC kan dauki dogon lokaci kafin a kammala, kuma sau da yawa suna jawo cece-kuce daga ‘yan siyasa da jama’a game da sahihancin binciken da tasirin siyasa a cikin lamarin.

A karkashin dokar Najeriya, duk wanda ake zargi yana da cikakken ‘yancin kariya da kuma samun damar kare kansa a kotu har sai an tabbatar da laifinsa. Wannan shi ake kira “babu wanda ake ɗauka da laifi sai an tabbatar”.

Sai dai a zahiri, irin wannan zargi, musamman idan ya shafi manyan jami’an gwamnati, kan iya girgiza martaba da amincewar jama’a ga mutum. Sau da yawa, zargin rashawa kan yi tasiri a siyasa, ya rage karɓuwa daga jama’a, kuma ya iya kawo tsaiko ga shirin neman wani mukami a nan gaba.

Masana harkokin doka da tsaron kasa sun bayyana cewa, ko da mutum ya sami nasara a kotu, tabon zargi na iya ci gaba da bin sa, musamman idan lamarin ya samu daukar hankali a kafafen yada labarai.

Follow Us