An Sasanta Sabani Tsakanin Manoma da Makiyaya a Dajin Shibdawa, Jihar Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23072025_075532_FB_IMG_1753257198707.jpg

KatsinaTimes

An cimma matsaya ta zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a dajin Shibdawa da ke yankin Barawa, karamar hukumar Batagarawa a Jihar Katsina.

Wannan sasanci ya biyo bayan ziyarar da sakataren gwamnatin jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya jagoranta a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025. Tawagar ta kai ziyara zuwa dajin domin duba halin da ake ciki tare da sasanta bangarorin da ke rikici.

A yayin ziyarar, an saurari koke-koken da manoma da makiyaya suka gabatar, sannan aka gudanar da tattaunawa mai zurfi wacce ta kai ga samun daidaito a tsakanin su bisa adalci da fahimta. Wannan mataki ya biyo bayan umarnin da Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya bayar na dakatar da duk wani aikin noma a cikin dazukan gwamnati da hanyoyin kiwo (Burtali), domin kauce wa rikici.

Bangarorin biyu sun bayyana godiyarsu ga Gwamna Radda da sakataren gwamnatin jihar bisa yadda suka gaggauta shiga tsakani da kuma kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Tawagar da ta kai wannan ziyara ta kunshi shugaban karamar hukumar Batagarawa, Hon. Yahaya Kawo; shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore a yankin, Alhaji Kuraye; Baturen ‘yan sanda na Batagarawa da sauran jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki.

Gwamnatin Jihar Katsina ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da zaman lafiya da magance rikice-rikicen manoma da makiyaya ta hanyar adalci da doka a duk fadin yankunan karkara na jihar.

Follow Us