Majalisar Dinkin Duniya Ta Nadi Farfesa Rabi’a Sa’id a Kwamitin Bincike Kan Makaman Nukiliya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes21072025_135202_Screenshot_20250721-144725.jpg

Majalisar Dinkin Duniya ta zabi Farfesa Rabi’a Sa’id daga Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) domin zama daya daga cikin kwararru 21 na duniya da za su yi bincike kan illolin amfani da makaman nukiliya.

Nadin Farfesa Rabi’a Sa’id – wadda kwararra ce a fannin kimiyyar nukiliya da sauyin yanayi – ya biyo bayan kafa sabon kwamitin na musamman karkashin kudurin MDD na 79/238, wanda zai duba tasirin makaman nukiliya ga lafiyar dan Adam, muhalli da tattalin arziki.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ne ya amince da nadin nata, inda ya bayyana cewa kwamitin zai mika rahoton binciken sa nan da shekarar 2027.

Farfesa Sa’id ta jaddada mahimmancin wakilcin nahiyar Afirka a irin wannan muhimmin dandalin tattaunawa, inda za a duba tasirin yaki da makaman nukiliya ga lafiyar duniya da sauyin yanayi. Ta ce aikin kwamitin zai bai wa kasashe kamar Najeriya damar bayyana matsayinsu da damuwarsu kan abubuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiya.

Masana da dama na kallon wannan matsayi a matsayin babbar nasara ga Najeriya, musamman wajen karfafa matsayin mata a fannin kimiyya da diflomasiyar duniya. Hakanan ana ganin nadin a matsayin wata gagarumar dama wajen karfafa rawar da Najeriya ke takawa wajen samar da mafita a matsalolin duniya da suka shafi lafiya, tsaro da kimiyya.

Farfesa Rabi’a Sa’id ta dade tana taka muhimmiyar rawa a fannin kimiyya a Najeriya da ma kasashen waje, musamman wajen ilimantar da al’umma kan sauyin yanayi da lafiyar muhalli.

Follow Us