KatsinaTimes
Marubuci kuma masani a harkar sadarwa, Farooq Kperogi, ya nemi gafarar Hajiya A'isha Buhari kan wani rubutun da ya wallafa a ranar 16 ga Yuli a shafinsa na Facebook da ya janyo ce-ce-ku-ce.
Rubutun mai taken “Aisha Buhari, Divorce, and Forgiveness Claim” ya bayyana wasu bayanai da suka danganci zargin saki da kuma neman gafara da ya ce shugaban marigayi Muhammadu Buhari ya nemi a roƙa masa kafin rasuwarsa.
A cikin wani bayani na nadama da ya fitar, Kperogi ya ce bai yi tsammanin illar da wannan rubutu zai iya yi wa Aisha Buhari da mutanen da ke kusa da ita ba. Ya bayyana wannan mataki nasa a matsayin “mummunar kura-kurai” da ya taɓa aikatawa a rayuwarsa.
“Wata majiya ta gaskiya ce ta ba ni wannan bayani, amma ba a tsara a bayyana shi a fili ba. Na yi kuskure da bayyana wannan magana ga jama’a,” in ji Kperogi.
Ya ce tsohon mai ba Uwargidar Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin jama’a, Alhaji Sani Zorro, ya tuntube shi yana tambayar sahihancin bayanan da ya fitar.
“Ba zan yi muhawara da Alhaji Sani Zorro ba, wanda ya bayyana matsayin Aisha Buhari cewa aurenta da marigayi mijinta bai mutu ba. Dama dai kamar yadda marigayi MKO Abiola ya faɗa, ba za a iya aske maka kai ba ba ka wurin,” in ji Kperogi.
Kperogi ya jaddada cewa Aisha Buhari ce kaɗai ke da cikakken iko da haƙƙin bayyana matsayin aurenta da marigayi shugaba Buhari, kuma dole ne a girmama abin da ta faɗa a matsayin gaskiya.
Ya ƙara da cewa, ko da bayanan nasa gaskiya ne, illar da suka haifar ya fi muhimmanci fiye da sahihancinsu. “Bai kamata na wallafa wannan bayani ba. Na karya ƙa'idodin ɗabi'a da ƙwarewar aikin jarida da na ɗauka darasi. Amma hakan ya nuna ni ɗan adam ne, kuma ina da kura-kurai,” in ji shi.
A ƙarshe, Farooq Kperogi ya miƙa cikakkiyar neman afuwa da nadama ga Hajiya Aisha Buhari, yana mai cewa: “Ina neman gafararki da zuciya ɗaya kan ciwon da wannan rubutu nawa ya haifar. Gaskiya ina matuƙar nadama.”