PDP Ta Katsina Ta Jaddada Haɗin Kai, Ta Shirya Tsaf Don Nasarar 2027

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13072025_164813_Screenshot_20250713-174723.jpg

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Katsina ta sake jaddada cewa tana nan da ƙarfi, da haɗin kai, kuma babu rarrabuwa a cikinta, a yayin wani babban taron kwamitin haɓaka shawara da aka gudanar a ranar Asabar, 13 ga Yuli, 2025, a sakatariyar jam’iyyar da ke Katsina.

Taron ya samu halartar shugabanni, dattawa, da magoya bayan jam’iyyar daga sassa daban-daban na jihar, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban jam’iyyar da shirye-shiryenta na gaba.

A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron, jam’iyyar ta bayyana cewa tana nan “cike da ƙarfi, ɗaya, kuma ba za a iya raba ta ba” karkashin jagorancin Sanata Yakubu Lado Danmarke. Taron ya kuma nuna cikakken goyon baya da amincewa ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa ƙarƙashin jagorancin mukaddashin shugaban jam’iyyar, Amb. Umar Ilya Damagun.

Kwamitin ya kuma nuna jin daɗinsa da irin gudunmuwar da manyan sassan jam’iyyar ke bayarwa, musamman Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC), Kwamitin Amintattu (BoT), da Ƙungiyar Gwamnonin PDP.

Haka zalika, taron ya yaba da aikin da Kwamitin Sulhu ke yi, tare da ƙarfafa mambobin jam’iyyar da su ba da haɗin kai domin samun daidaito da zaman lafiya a cikin gida.

Game da siyasar ƙasa, PDP ta nesanta kanta da kowace irin haɗin gwiwa da ba ta bi sahalewar shugabancin jam’iyyar ba, tana mai kira ga ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da su shigo cikin jam’iyyar domin ceto ƙasar daga “zaluncin mulkin APC.”

Dangane da zaɓen 2027, jam’iyyar ta bayyana aniyarta na ƙara zage damtse domin samun nasara a matakai daban-daban a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Sanarwar ta samu sa hannun Shugaban PDP na Jihar Katsina, Hon. Muhammad Nura Amadi

Follow Us