KADAN DAGA RAYUWAR HAJIYA BINTA MUHAMMAD RIMI.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes23052025_205301_IMG-20250523-WA0337.jpg


Allah ya yima hajiya Binta Muhammad Rimi.
Hajiya binta wadda akafi sani da hajiya kangiwa Rasuwa. Wadda  Diyace ga marigayi Alhaji Malam sabo makera (Dan Sarkin makera na Rimi) 

An haifeta a unguwar makera a shekara ta 1932. Ta bangaren mahaifiyar ta kuma tana daga ɓangare Malam Muhammad modda babban malami kuma attajiri wanda yake kakane ga su Alhaji muntari lawal, Alh ali Angas da prof Naaliya da Alhaji Hamisu Gambo Dan lawan katsina.

Tayi rayuwa a garin Rimi inda daga bisani ta auri Alh Muhammad najaeh dayane daga cikin jikokin shantali Alu .

Hajiya ta haifi ƴa'ƴa tara 9 maza 3 mata shidda.
Sune
1. Comrd Bilyaminu Mohammed Maza wajen Katsina.
2. Alh surajo Muhammad 
3. Alh sanusi Muhammad (sukora)
4. Hajiya Hauwa
5. Hajiya Husaina
6. Hajiya Rabiatu (jummai)
7. Marigayiya Hajiya amina
8. Hajiya maryama 
9. Hajiya Lubabatu.

Tana da jikoki maza da mata Wanda adadinsu mukai guda 72.

Follow Us