Sani Mai Katanga Ya Ƙara Lashe Gasar Ɗaukar Hoto Ta Duniya
- Katsina City News
- 18 Sep, 2023
- 949
Ɗan asalin jihar Kano Sani Maikatanga ya ƙara lashe gasar ɗaukar hoto ta Duniya.
Daga Barr Nuraddeen Isma'eel Zariya.
“Malam Muhammad Sani wanda aka fi sani da Maikatanga shi ne ya lashe gasar ɗaukar hoto ta duniya mai taken ‘Wiki Loves Africa 2023’ Maikatanga ya nuna matukar jin dadinsa da wannan nasara da ya samu kasancewarsa dan asalin jihar Kano.
“Mai ɗaukar hoton dai ya samu lashe gasar ne da wani hoto da ya dauka a jihar Jigawa a karamar hukumar Auyo a lokacin da aka samu ambaliyar ruwa.
“Maikatanga hoton dai ya yi fice matuƙa wurin ƙwarewa fagen iya ɗaukan hoto, wanda ta kai ga harta sashin Hausa na BBC suna amfani da hotunansa da daman gaske.”
Bugu da ƙari Muhammed Sani Maikatanga ya sha amsan kyaututtuka ta karramawa daga gwamnatoci, ƙungiyoyi, da daman gaske ba adadi, kuma ba wannan bane karo na farko ba a lashe gasar ɗaukan hoto da yayi na duniya.
“Sani Maikatanga ya taka ƙasashe daban-daban a dalilin sana'ar ɗaukar hoto, bihasalima yakaima sarakuna, biki na masu hannu da shuni, Makarantu da suka haɗa da kamar jami'oi, kwalejoji, da dai makamantansu a fadin Afrika ya na amsa gayyatar su domin ya yi aiki na wannan sana'ar nashi.