Tinubu Ya Girmama Sule Lamido a Bikin Ƙaddamar da Littafin Rayuwarsa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13052025_205928_FB_IMG_1747169678352.jpg




Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yabawa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, a wani biki na musamman da aka gudanar a Abuja domin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai take Being True to Myself.

A sakon da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya isar a madadin Shugaban Ƙasa a wajen taron da aka gudanar a Cibiyar Taro ta NAF da ke Abuja, an bayyana Lamido a matsayin ɗan siyasa mai aƙida, jarumtaka da jajircewa wajen kare dimokiraɗiyya a Nijeriya.

Minista Idris ya ce, “Wannan taro ba kawai ƙaddamar da littafi ba ne, amma bikin rayuwa ne da jarumtaka da kuma daidaito na siyasa.” Ya kara da cewa kodayake Lamido na daga cikin manyan ‘yan adawa kuma mai sukar gwamnati, amma bai gushe ba wajen bada gudunmawa ga siyasar ƙasa.

Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana mutunta siyasar da ke buɗe ƙofa ga ra’ayoyi daban-daban, inda kowane ɗan ƙasa ke da damar yin tasiri a tattaunawa kan makomar ƙasa, ba tare da la’akari da jam’iyya ba.

A cewar Idris, rubuta littafin ya ɗauki fiye da shekaru goma, kuma Lamido ya cancanci yabo bisa irin rawar da ya taka wajen adana tarihin siyasar Nijeriya. “Taken littafin ya dace da halin Lamido – mutum ne mai gaskiya da tsayawa akan aƙidarsa,” in ji shi.

Ministan ya bukaci ɗalibai, malamai, ‘yan jarida da ‘yan siyasa da su karanta littafin don amfana daga zurfin fahimta da gogewar da ke cikinsa.

Game da gwamnatin Tinubu, Idris ya ce matakan sauyi da aka ɗauka – kodayake masu tsauri ne – sun fara nuna tasiri wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa. Ya ce: “Shugaba Tinubu na da hangen nesa da ƙarfin hali wajen ɗora ƙasar a kan turbar ci gaba.”

Kan batun tsaro, Ministan ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa na aiki tukuru don kare rayukan ‘yan ƙasa da ƙasar gaba ɗaya, yana mai jaddada bukatar a yaba da sadaukarwar da dakarun tsaro ke yi.

Haka zalika, ya ce sabbin dokokin haraji da Shugaban Ƙasa ya gabatar na nufin ƙara kuɗaɗen shiga ba tare da ƙara wa talakawa nauyi ba.

Idris ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu na karɓar suka mai amfani da zai taimaka wajen kyautata mulki, amma ba zai bari hakan ya karkatar da shi daga aikata abin da ya dace ba.

Taron ya samu halartar fitattun ‘yan siyasa daga ɓangarori daban-daban na ƙasa, inda aka yaba da irin gudunmawar da Sule Lamido ya bayar wajen gina dimokiraɗiyya a Nijeriya.

Follow Us