Mazauna Gambarawa a Katsina Sun Samu Fitilar Sola Bayan Neman gudunmawa ga shugaban karamar hukuma

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13052025_202503_FB_IMG_1747167738305.jpg



Daga Wakilinmu

Mazauna unguwar Gambarawa da ke cikin birnin Katsina sun samu farin ciki bayan bukatar su na samar da fitilar wutar sola ta samu amincewa daga shugaban karamar hukumar Katsina, Honourable Isah Miqdad AD Saude.

Al’ummar yankin, da ke dibar ruwa a wani wuri da ya hada sama da unguwanni biyar, sun bayyana damuwa kan rashin haske da ke jefa su cikin barazana musamman da dare. Wannan ya sa suka bijiro da bukatar a samar musu da fitilar sola don karfafa tsaro da inganta rayuwarsu.

Shugaban karamar hukumar Katsina, Honourable Isah Miqdad, ya ziyarci wurin ta hannun wakilin sa, tare da tabbatar da cewa akwai bukatar gaggauta sanya fitilar wutar sola a wajen da fiye da mutum dubu daya ke amfani da shi wajen dibar ruwa, komai dare.

A cewar Isah Miqdad, wannan aiki na daga cikin nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaba, kuma yana da alhakin tabbatar da jin dadin al’umma. Ya ce nan bada jimawa ba, sauran unguwannin da ke ƙarƙashin karamar hukumar Katsina za su ci gajiyar irin wannan gudunmawa ta fitilu domin kara inganta tsaro.

'Yan unguwar sun nuna farin ciki da godiya ga wannan mataki, tare da fatan alheri da nasara ga sabon shugaban karamar hukumar, Honourable Isah Miqdad.

Follow Us