Jinjina ga shugaban Jamiar Tarayya da ke Dutsimma Prof Armayau Hamisu Bichi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12022025_122034_images (6).jpeg

Daga Bilkisu Yusuf Ali

Hukumar Zartarwa ta Jami'ar Gwamnatin tarayya ta Dutsimma da ke jihar Katsina ta yi abin da ya dace. 

Kwana biyu bayan futowar wata sanarwa kan tsayar da duk wani abu da ya shafi Darikar Tijjaniyya a masallacin makarantar, sai Tijjanawa suka fara kiraye-kiraye kan hukumar makaranta ta shiga lamarin don kowanne dan kasa yana da 'yancin gudanar da ayyukansa na addininsa da akidarsa. Wannan ya ja hankalin hukumar makarantar bayan ta ji ta bakin kowanne bangare a karshe ta amince tare da sahalewa Tijjanawa yin ayyukansu da ya shafi darikar Tijjaniyya a masallacin Library din jamiar. 
Hakika shugabar jamiar Gwamnatin Tarayya ta FUDMA Farfesa Armayau Hamisu Bichi mutumin kirki ne da yake son cigaban kowanne dalibi da ke jamiar. Yayin zantawar da wakilanmu suka yi sun nuna yadda yadda ya damu da ya ji wannan sabanin ya bullo. VC na son zaman lafiya"

Follow Us