Sakataren Dindindin Da Wasu Biyar Sun Shiga Hannu Kan Zargin Almundahanar Naira Miliyan 136, a Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

Hukumar Jin Korafe-Korafe da Yaƙi da Cin Hanci da rashawa ta Jihar Katsina ta kama Sakataren Dindindin na Hukumar Kula da Ayyukan Ƙananan Hukumomi, Alhaji Muheeb Ibrahim Bamidele, tare da wasu mutane biyar bisa zargin karkatar da kuɗi har naira miliyan 136.  

Bayanan da aka samu sun nuna cewa an yi almundahana da kuɗaɗen ne daga asusun Sashen Banking da Finance, wanda shi ne Bamidele ya shugabanta a baya. Hukumar ta ce bincike na ci gaba don gano cikakken gaskiyar lamarin tare da tabbatar da adalci ga al’ummar jihar.  

Sakataren Hukumar Korafe-Korafen, Dakta Jamilu M. Abdulsalam, ya bayyana cewa za a ci gaba da gudanar da bincike a kan wannan badakala, tare da tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka samu da hannu.  

Hukumar ta yi alkawarin sanar da jama’a sabbin bayanai da zarar bincike ya kammala.

Follow Us