Fage da Mai Kilago! Daga farfesa Abdallah uba adamu
- Katsina City News
- 26 Jan, 2025
- 53
Tasowar mu a cikin gari, kwarin gogau na daya da ga cikin wuraren da muke tsoro ƙwarai da gaske. Dalili kuwa shi ne an ce rafin Ƴar Fari da ya keta ya bi ta bayan tsohuwar silimar Plaza, na ke jin kuma daura da silimar Orion, nan ne inda Mai Kilago ke zama. Aljani ne a ruwa. Kuma ya fi son ƙananan yara, baran ma waɗanda suke bulɓul. Da zarar yaro ya je Ƴar Fari don wanka, to tabbas Mai Kilago zai cinye shi. Baya cinye manya, sai yara, saboda haka in ma wanka yaron ke son yi, to idan Mai Kilago ya gan shi da babba, sai ya kyale shi.
Ƴan ɗaukan hoton zamanin har hoton sa suka samo suna yawo da shi ana saya. Da gani tabbas Mai Kilago abin tsoro ne. Ga shi garjejen ƙato, kuma don girma ma baya iya tashi, rarrafe ya ke yi.. An jima ana yawo da wannan hoton, kuma mun jima muna tsoron ratsa rannan yafin. Shi ya sa mu a zamanin mu, muke ganin ƴan Fage a matsayin jarumai saboda su kusa da Mai Kilagon suke, amma ko gezau a jikin su!
Da ilimi ya yawaita, a hankali muka gane babu wani aljani mai suna Mai Kilago. Hoton da ake yawo da shi na Mai Kilago, wani zanen barkwanci ne wanda shahararren mai zane a Ingila, William Blake, ya yi na Nebuchadnezzar, daya daga cikin sarakunan birnin Babylon. A yanzu dai zai zama a cikin Iraq, kusan kilomita 85 daga Bagadaza (misali nisan daga Kano zuwa Kwanar Ɗangora). Har yanzu akwai ɓurɓushin dagargadeddn birnin (ruins) inda ake zuwa yawon buɗe ido dan ganin yadda tarihi ya kasance.
Nebuchadnezzar dai gawurtaccen sarkin Babylon ne daga c. 634–562 BCE. Mai Kilagon da William Blake ya zana ya nuna fahimtar shi Blake din da cewa Nebuchadnezzar ya haukace a kan ganiyar mulkin sa. Ya zama kamar wanda a ke farautar sa, idon sa cike da tsoro. Hakan ta faru ne saboda irin mulkin da ya yi wa Babylon mai tsauri, kuma Allah Ya jarab ce shi da ibtila’o’i. Azabar da zata biyo shi, wanda har a Injila an yi labarin sa, shi Blake ya nuna – mu kuma muke tsorata shi.
To ka ga, ta haka tsoron Mai Kilago a Fage ya sa muka samu wani ilimin tarihin duniya, saboda tun da na tuna da wannan hoton sai da na zaƙulo tarihin!
Fage! Fagen Rogo. Fagen Daga. Fagen Tarihin Duniya!
Ga dai Mai Kilago a ƙasa!