Gwamnatin Jihar Katsina ta kammala gyaran rukunin dakunan kwanan dalibai da sake ginin bangon da ya zagaye Kwalejin horas da Jami'an tsaro wato Sibil Difens dake kan hanyar Batsari a nan Katsina.
- Katsina City News
- 24 Jan, 2025
- 66
Da yake hannanta gineginen ga Hukumar Kwalejin a madadin Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, Sakataren Gwamnati, Alhaji Abdullahi Garba Faskari ya yaba da ingancin aikin da aka gudanar.
Sakataren Gwamnatin wanda Daraktan watsa labarai na ofishinsa Abdullahi Aliyu Yar'adua ya wakilta, ya ce Gwamna Dikko Radda ne bada umurnin a gudanar da aikin a sakamakon koken da ya samu daga Kwamandan Kwalejin akan halin tabarbarewar dakunan kwanan da kuma faduwar wani bangare na katangar da ta kewaye Makarantar, wanda ke bukatar kulawar gaggawa.
Ya ce, akan haka Dr. Dikko Umaru Radda ya amince da a baiwa Ma'aikatar Ayyuka ta jiha dama ta aiwatar da gyaregyaren ta hanyar yin aikin da kanta.
Sakataren Gwamnatin ya yi kira ga shugabannin Kwalejin da su tabbatar ana amfani da dakunan da ma sauran kayayyakin da aka tanada don kyautata yanayin horo da horaswa da ke gudana a Kwalejin.
A jawabinsa, Babban Sakatare na Ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri, QS Umar Isiyaku Rugoji ya ce aikin gyaran da Makarantar ke bukata wanda zai lashe kudi sama da # Miliyan Dari an kasa shi gida uku, don haka yanzu an gama da kashi na farko.
Da yake karbar takardun mika gineginen, Kwamandan Kwalejin Bishiri I. Saulawa ya jinjina ma Gwamna Dikko Umaru Radda akan wannan katafaren aiki da ya wa Kwalejin.
Bishiri Saulawa ya bayyana Gwamna Dikko Radda a matsayin babban jigon Makarantar wanda bai taba nuna gajiyawa ba a duk lokacin da ta nufe shi da bukatun da suka sha karfinta.
Ya sha alwashin cewa Hukumar Kwalejin za tsare ta tabbatar dalibai da sauran Jami'an Kwalejin sun kare kayayyakin da aka samar masu daga barnatarwa.
Daraktan sashen ginegine na Ma'aikatar Ayyuka, Injiniya Muhammed Sada Abdullahi ya shawarci Hukumar Kwalejin da ta kara kula da gineginen Makarantar sosai ta hanyar yin feshin maganin kwari akalla sau uku a shekara saboda a kawar da gara da sauran kwari dake lalata gineginen Makarantar.
Daga cikin wadanda suka shedi mika gineginen da Gwamnatin Jihar ta gyara akwai Mukaddashin Daraktan Tsaro a ofishin Gwamna, Alhaji Hamza Audi Kofarbai tare da manyan Jami'an Kwalejin bada horon ta Sibil Difens.