KASSAROTA Ta Nesanta Kanta Daga Ayyukan Zamba ga Wasu Masu Yi da Sunan Hukumar
- Katsina City News
- 22 Jan, 2025
- 170
KASSAROTA Ta Nesanta Kanta Daga Ayyukan Zamba ga Wasu Masu Yi da Sunan Hukumar
Katsina Times
Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA) ta yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa wasu mutane suna fakewa da sunan jami’an hukumar domin aikata miyagun ayyuka a sassa daban-daban na jihar. Rahotanni sun bayyana cewa wadannan mutanen suna tsayar da direbobi da masu babura suna musu karya, suna karbar kudade ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma karbe ababen hawa ko kakabawa mutane tara ba bisa ka’ida ba.
Hukumar ta bayyana karara cewa, ba ta da hannu a irin wadannan ayyuka, kuma tana tabbatar da cewa mutanen da ke yin hakan ba jami’an KASSAROTA ba ne. Wannan dabi’ar ya ci karo da ka’idojin aiki, ladabi, da tsare-tsaren hukumar.
KASSAROTA ta jaddada aniyarta ta tabbatar da tsaron dukkan masu amfani da hanya a jihar. Don haka, hukumar ba za ta lamunci cin hanci ko wata irin barazana ga jama’a ba. Ana kira ga al’ummar jihar su rika kai rahoton duk wani mutum da ke da abin zargi ko kuma masu fakewa da sunan jami’an KASSAROTA ga hukumomin tsaro mafi kusa.
Hukumar ta kuma yi kira ga shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki su taimaka wajen yada labarai game da wadannan masu zamba, tare da hada kai da hukumomin tsaro domin cafke su.
KASSAROTA ta fahimci kalubalen tattalin arziki da jama’a ke fuskanta, kuma tana tabbatar wa jama’a cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin gaskiya da kwarewa domin ci gaban jihar Katsina.
Wannan sanarwa ta fito daga bakin Babban Daraktan KASSAROTA, Manjo Garba Yahaya Rimi (Rtd.), ta hannun jami’in hulda da jama’a, Marwana Abubakar Kofar Sauri.