Jami'an Tsaro A Abuja Sun Kama 'Yan jihar Katsina Da Ballar Kayan Nauyi
- Katsina City News
- 07 Jan, 2025
- 254
Jami'an tsaron Civil Defiance a karshen mako, sun kama wasu mutane biyar da ake zargi da fasa tare da sace kayan gwamnati kan Titin Constitutional, Yankin Central Area na birnin Abuja.
Wadanda aka kama sun hada da Nafiu Ibrahim, shekaru 19 daga karamar hukumar Kurfi ta Jihar Katsina; Shefiu Sadiq, shekaru 21 daga Kurfi; Yahaya Musbau, mai shekaru 24; Mohanzam Muktar, mai shekaru 20; da Yunusa Ma’aruf, amai shekaru 19. Dukansu ‘yan asalin karamar hukumar Kurfi ne ta Jihar Katsina.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da murfin rami guda biyu, wayoyin lantarki masu sulke na karkashin kasa, diga biyu, da motoci biyu—Toyota Carina da Toyota Corolla—wadanda aka yi amfani da su don daukar kayan da suka sace.
Haka zalika, an kama wasu biyu da ake zargi da lalata karafunan siminti na magudanan ruwa kusa da Fadar Shugaban Kasa. Wadanda aka kama sun hada da Haruna Yahaya, mai shekaru 20 daga karamar hukumar Kura ta Jihar Kano, da Haliru Sanusi, mai shekaru 22 daga karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina.
A cewar wata sanarwa, an kama wadanda ake zargi bayan jami’an NSCDC sun yi musu kwanton bauna a lokacin da suke kokarin lalata da cire murfin ramuka da wayoyin lantarki a kan Titin Constitutional, Yankin Central Area na Abuja, cikin tsakar dare.