'Yanbindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Tare Da Jikkata Hudu Hanyar Jibiya Zuwa Garin Katsina
- Katsina City News
- 25 Nov, 2024
- 263
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
'Yanbindiga sun kai hari ga motar fasinjoji a hanyar Jibia zuwa Katsina a ranar Lahadi, inda suka kashe wani fasinja, yayin da Mutum hudu suka jikkata.
Wani da abin ya faru a gaban sa, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda muhimmancin lamarin, ya shaida wa wakilinmu a ranar Lahadi cewa an kai harin ne da nufin yin garkuwa da fasinjojin.
Sai dai, a cewar majiyar, sojoji sun kai dauki cikin sauri, sun ceto wadanda abin ya shafa, sannan suka kwashi wadanda aka jikkata da wanda ya mutu zuwa Asibitin Koyarwa na Jibia.
Ya ce, “A yau da maraice, 'Yanbindiga sun kai hari a hanyar Jibia zuwa Katsina, a yankin kauyen Dan Arau, wanda ke kusa da garin Magama a karamar hukumar Jibia, inda suka bude wuta kan wata mota dauke da fasinjoji daga Kasuwar Jibia.
“A cikin harin, fasinjoji biyar ne aka harba, daya ya mutu nan take, yayin da hudu suka ji raunuka daban-daban na harbin bindiga kuma aka garzaya da su asibiti.
“Muna godiya ga gaggawar martanin hadin gwiwar sojoji da ya sanya da sanya 'yanbindiga guduwa tare da sakin wadanda aka yi garkuwa da su.” Inji mazauna yankin.
Kakakin rundunar 'Yan Sanda na Jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin.