Gwamnan Katsina Ya Bai wa Dalibin Jami'ar UMYU Mai Sakamakon Digiri Na Farko Aiki Kai Tsaye
- Katsina City News
- 15 Nov, 2024
- 335
Maryam Jamilu Gambo
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya bai wa Sham'unu Ishaq, dalibi mai digiri na farko daga Jami'ar Umaru Musa Yar’adua, aikin kai tsaye bayan an gano yana sayar da ruwa domin tallafawa iyayensa.
Bayan ya samu labarin halin da Sham'unu ke ciki, Gwamna Radda ya umarci Mataimakinsa na Musamman kan Harkokin Dalibai, Hon. Muhammad Nagaske, da ya bincika gaskiyar bidiyon da ya karade kafafen sada zumunta.
Binciken ya tabbatar da cewa Sham'unu Ishaq ya kammala karatunsa na digiri na farko a fannin Education/Biology da sakamako mafi kyau a shekarar 2021/2022. Wannan shaida ta samu tabbaci daga Mataimakin Shugaban Jami’ar.
Sham'unu, wanda ya kammala aikin bautar kasa (NYSC) a Jihar Taraba, ya shiga sana’ar sayar da ruwa don cike bukatunsa da na iyalinsa.
"Ya kamata a yaba wa hazikai ba a bar su cikin wahala ba," in ji Gwamna Radda yayin bayar da umarnin tabbatar da daukar Sham'unu aiki ta hannun Shugaban Ma’aikata.
Ya kara da cewa, "Gwamnatinmu za ta ci gaba da gano hazikan matasa da za su taka rawar gani wajen ci gaban jihar Katsina."
Wannan matakin ya yi daidai da kudirin Gwamna Radda na ganin an daukaka harkokin ilimi da kuma ba wa kwararrun matasa dama.
A watan da ya gabata ma, ranar 12 ga Oktoba, 2024, Gwamnan ya bayar da aikin kai tsaye ga dalibai tara da suka yi fice a Kwalejin Ilimi ta Isah Kaita dake Dutsinma. Haka zalika, a ranar 26 ga Mayu, 2024, Gwamnan ya dauki dalibai tara da suka yi digiri na farko daga Jami'ar Umaru Musa Yar'adua a bikin kammala karatu na hadin gwiwa na jami'ar.
"Gwamnatinmu ta fahimci cewa makomar Jihar Katsina tana hannun matasanmu masu hazaka," in ji Gwamna Radda.
"Za mu ci gaba da samar da damar da za su ba wa matasa damar amfani da iliminsu da fasaharsu domin amfanin al’umma."