KASAR KATSINA, KAMIN ZUWAN TURAWA.

top-news

  A Tarihance zaa  Katsina kamin zuwan Yan mulkin mallaka ta rutso da zamani kamar guda ukku. Na farko alokacin Maguzanci, Wanda ya faro tun kafuwar shi har zuwa karshen shi lokacin Sarki Sanau. A wannan lokacinne ake bautar iskoki, da Tsahe- Tsahe da sauransu. Addinin musulunchi bai Kai ga  bayyana ba. Masu mulki da  Yan Kasuwa da Talakawa kowa yayi imani da Aljanin shi, kuma a kanshi ya dogara. Misali Sarakunan Durbi Takusheyi Tarihi ya nuna duk Maguzawane masu bautar Iskoki da sauransu. 


 2. Said kuma bangare na biyu  na  Tarihin Katsina kamin zuwan Turawa shine na  zuwan musulunchi a Katsina, Wanda ya faro daga mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Korau(1348).  A wannan lokacinne musulunchi ya kunne Kai a Katsina kuma ya Fara Fada da bautar Iskoki da    Tsahi. A  wannan lokacinne kasuwanci ya Kara bunkasa a Katsina, Garin Katsina ya Kara bunkasa saboda shigowar baki yan Kasuwa, misali Unguwar YanSiliyu, da Sararin Tsako, da Albaba, da sauransu duk bakin Yan Kasuwa suka kafasu a lokacin mulkin Habe. Hakanan kuma Shariar musulunchi da ilimin addini ya yawaita a lokacin.  A karshen karni na sha shidda ( K16) Kasar Katsina  ta  fitar da manyan Malaman addinin musulunchi wadanda sukayi ficce a duniya, daga cikin su akwai Sheik Muhammad B. Masani, Albarnawi Alkatsinawi,  Wanda akafi sani da Danmasani, ( 1595-1667). Dan Masani asalin kakannin shi mutanen Borno ne Amma shi an haifeshi a Katsina a Unguwar Masanawa. Danmasani yayi Sharhi akan littafin Ishiriniyya ta alfazazi,  da sauran rubuce rubucen da yayi. Akwai kuma As Sheik Muhammad Alfulani Alkatsinawi, Wanda aka Haifa a Kurmin Yanranko. Alkatsinawi yayi karatu a Katsina, daga baya yaje kasar Misra( Egypt), daga Misranne ya wuce yayi aikin Hajji, acan Makkan  ya rubuta littafi akan ilimin Taurari ( Astronomy). Ya dawo Misra inda yayi abota da wani babban Malami Mai suna Sheik Hassan Aljabarti, Alkatsinawi ya rasu a Egypt kuma acan aka rufeshi, daga cikin rubuce rubucen shi akwai Al- Durum Al- Manzum da sauransu Wanda ya kammalasu a Egyt a cikin shekarar 1773 zuwa 1774. Da sauransu. 

   A dai dai lokacin mulkin Habenne kuma aka Gina Masallacin Gobarau a Katsina a lokacin mulkin Sarkin Katsina Muhammad Korau (1348-1398). Wannan kuma ya biyo bayan ziyarar da Sheik Almaghili ya kawo Katsina, Almaghili ya zo Katsina daga That ta Kasar Algeria. Ya bada shawarar a Gina Masallacin Gobarau Wanda Masallacin daga baya ya Zama babbar Jamia ta koyar da ilimin addinin Musulunchi bawai a Kasar Katsina a gaba dayan Kasar Hausa.  Hakanan kuma  a cikin karni na goma Sha shidda ne ( K16).  Tafsirin Jalalaini ya yawaita a Kasar Katsina.  Shi wannan Tafsirin Sheik Jalaluddin Alsuyudi ya Fara Rubutashi sai kuma Sheik Jalaluddin Almuhalli ya kammalashi, shiyyasa ake ce msshi Tafsiril Jalalaini. Da sauran ilimin addini kamar Hadith da Fikihu da sauransu duk sun yawaita a wannan lokacin. 

3. Sai bangare na ukku na Tarihin Katsina kamin zuwan Turawa shine a bulluwar Jihadi na karni na   sha Tara (K19). Wanda a Katsina  masu Jihadi a karkashin Jagorancin Malam Ummarun Dallaje sun kwace mulki daga Sarakunan Habe acikin shekarar 1806. Wannan ya jawo aka kafa mulki irin na Tarayya ( Emirate system). Aka kafa gwamnatin  musulunchi wadda take ansar Umarnin ta daga babbar hedikwata ta Sokoto ( Sokoto Chaliphate). A wannan lokacin an Kara karfafa Shariar Musulunchi a Katsina, ilimn addini da Makarantun musulunchi sun yawaita. Shuwagabanin Jihadin sun Gina Masallatai, an gina Masallacin Jumaaa na biyu a Katsina Wanda yake anan shiyyar Galadunchi da sauransu. 

Alh. Musa Gambo Kofar soro.