BIKIN NADIN SABON SARKI, BISA AL'ADAR BADAWA.

top-news

  A kasar Bade masu zaben SARKI da manyan Fafawa su suke yin Nadi. Akwai wasu al'adu  wadanda ake yi a wannan lokaci daya bayan daya. Da zarar an tabbatar da sabon Sarkin Bade, za a shiga tanade-tanaden kayan Nadi na Gargajiya da sauran shirye-shirye. Daga cikin kayan al'ada da ake tanada akwai:. 

1. Tabarma Fara ( Malfa) wadda a kanta ne SARKI zai zauna. 

2. Bakar Riga ( Riga baka Mai Walkiya)

3. Farar Riga ( Ganduram)

4. Alkyabba Fara

5. Dara ja

6. Rawani

7. Takobi

8. Wukar yanka

9. Takalmi ( Bulka)masu kama da fade

10. Fartanya, alamar Sarkin Noma

11.  Danyar Kaba, alamar zaman Lafiya

12. Sandar mulki ( Dogzagi) wadda ake sassakawa ta itace ayita madaidaiciya, a yi mata Kai (dunkule) daga kasa, maimakon ayi shi daga  sama. 

       Idan sabon Sarkin Bade ya halarci filin Nadi, zaa Fara zaunar dashi ne kan tabarma Fara wadda aka shirya masa. Daga Nan,  sai a sa masa Rigar Kore Mai Walkiya sai a kawo Rigar Bulluma, a Dora masa  kan wannan koriyar, sannan a.dauko alkyabba a yafa masa, sai Galadima ya nada masa Rawani. 

  Bayan da aka Gama nadin Rawani sai Limami yayi addu'a. Sannan Magudiya tayi guda sau (3). Mai kada Tambari ya kadashi har sau ukku. Shima Mai Ganga gabade, doguwar Ganga ya kadata sosai. Sauran makadan SARKI kamar yan algaita, da Kakaki da sauransu suma su ciga gaba da aikinsu. Bayan an natsu sai Galadima yazo ya kama kafadar SARKI, ya kaishi inda zai zauna, Don karbar bai'a. Daga Nan sai mutanen SARKI su Fara gaisuwa da  mubayaa. 

1. Galadima zai yi jagorancin masu zaben SARKI suzo su jaddadama Sabon SARKI mubayaarsu. 
2. Masu Sarautun Gargajiya da manyan Fadawa suma su kawo gaisuwarsu. 

3. Yan jinin Sarauta su kawo bai'a. 

4. Bayin SARKI su kawo mubayaa

5 Da sauran Kungiyoyin rukunan Fada. 

6. Sauran Kungiyoyin  Dagattai da Maaikata  da Yan Kasuwa  da sauran Talakawa duk zasu  zo kungiya bayan Kungiya. 

   Wadannan sune muhimmai  daga cikin al'adun Nadin Sabon Mai Bade. 

MA'ANAR WASU KALMOMI DAGA HARSHEN BADAWA

1. BADE.  Kabila  ce wadda take zaune a wata ayyananniyar  farfajiya da ake Kira Kasar Bade, wadda ke Gashua cikin Jihar Yobe ta yanzu. 

2. BADAWA.  Sunan mutanen dake zaune a Kasar Bade
3. BABADE. Mutumen Kasar Bade. 

4. BADANCI. Yare ne na HARSHEN BADAWA kamar Barbanci, da Bolanci da Fulatanci da Hausa da sauransu. 

5. DUGUN.  Sunan Jagoran BADAWA kenan da HARSHEN BADANCI kuma yana a matsayin shugaba ko Mai Unguwa ko Dagaci. 

6. Gorgorom. HARSHEN Badancine dake nufin Daji Mai Duhu. 

7. LAWAN.  Uban Kasa kenan ko Hakimi. Kalma ce ta Barbanci. 

8. MAI. Sarki ne a babban gari ok birni ko alkarya. Yawanci shine ake Kira Sarki mai wukar yanka bayan zuwan Turawa a 1903.  Mai Kalma ce ta Barbanci, BADAWA suka arota daga Barebari, suka rika Kiran Sarkin su da MAI. 

9. MAINA.  Itama Kalmar Barbancice da take nufin  Dan Sarki. 
10. MAIRAM. Tana nufin Yar Sarki. Mace Yar Jinin Sarauta wadda ta fito daga cikin yayan Sarki ana kiranta " MAIRAM" da HARSHEN Barbanci. 

Alh. Musa Gambo Kofar soro.