Takaddamar Daliban Zamfara a Jami'ar Cyprus: Gwamnati na Ci Gaba da Yunkurin Shawo Kan Matsalolin Kuɗin Karatu
- Katsina City News
- 03 Nov, 2024
- 293
A ranar 29 ga watan Mayun 2023, Gwamna Dauda Lawal ya karɓi jagorancin gwamnatin Zamfara daga wadda ta gaza biyan kuɗaɗen jarabawar ɗalibai har na tsawon shekaru uku, abin da ya hana ɗaliban jihar damar ɗaukar jarabawar WAEC da NECO.
Daga cikin matsalolin da gwamnatin ta gada akwai rashin biyan kuɗaɗen karatu na ɗalibai masu karatu a ƙasashen waje, ciki har da Cyprus da India. A halin yanzu, ɗaliban Zamfara da ke karatu a India sun kammala karatunsu, kuma gwamnati na shirya dawowarsu gida. Har ila yau, gwamnati ta kwaso ɗaliban Zamfara daga Sudan sakamakon yaƙin da ake fama da shi a ƙasar, tare da ɗaukar nauyin jarabawar ƙarshe ga ɗalibai 14 masu karatun Nas.
Sai dai, matsaloli na ci gaba da kunno kai a Jami'ar Cyprus duk da kokarin gwamnatin Zamfara na warware su. A ranar 12 ga Nuwamba 2023, gwamnatin jihar ta biya jami’ar Naira miliyan 84.7, sannan a ranar 14 ga Nuwamba an sake tura Naira miliyan 30.9. Duk da haka, jami'ar Cyprus ta ƙi amincewa da tawagar gwamnatin jihar domin tattauna batutuwan ɗalibai. Bayan matsin lamba daga ofishin jakadancin Nijeriya a Turkiyya, jami’ar ta amince da ziyarar tawagar a watan Yuni 2024.
Gwamnan jihar ya tura tawagar mutane uku zuwa Cyprus domin bincike kan kuɗin da jami’ar ke bin jihar da kuma yanayin karatun ɗaliban Zamfara. Bayan ganawa da shugaban jami’ar, tawagar ta bayyana damuwa kan yanayin da ɗaliban suke ciki, ciki har da rashin rijistar ɗalibai da hana abinci ga ɗalibai da aka kore daga ɗakin kwanan su.
Tawagar ta kuma gano rashin daidaito a bayanan kuɗaɗen bashi na ɗaliban da jami’ar ta bayar. An bayyana bambanci mai yawa tsakanin jimlar basussuka da jami’ar ke ikirarin ana bin jihar. Ofishin Jakadancin Nijeriya a Turkiyya na ci gaba da matsa lamba don ganin an samar da takardun da za su ƙare wannan rikici.