Bata-Gari Sun Addabi Mazauna Rukunin Gidajen Sardauna a Katsina
- Katsina City News
- 03 Nov, 2024
- 792
Auwal Isah (Katsina Times)
Wasu bata-gari da ake zargin 'yan fashi da makami ne sun farmaki Rukunin Gidajen Sardauna (Sardauna Estate, Katsina) a daren jiya, Asabar.
Wani mazaunin rukunin gidajen, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya shaida wa KatsinaTimes ta wayar tarho cewa da misalin karfe 3:00 na dare, wasu mutane dauke da makamai kimanin su talatin sun kutsa kai cikin gidajen. Sun fara da kama wani maigadi daga cikin rukunin gidajen, suka daure shi tare da kwashe masa dukkan kudaden sa.
Mazaunin ya ci gaba da bayyana cewa daga nan sai suka rika bi rukuni-rukunin gidaje, inda suka kutsa wani gida a 'Matazu Road.' An jiyo matar gidan na kururuwar neman taimako, kuma wani makwabcinta da ya zo kawo dauki an ce 'yan fashin sun sassare shi, sannan suka shiga gidansa suka kwashe dukiyarsa, suka bar shi cikin jini.
Wasu shaidu mazauna rukunin gidajen sun tabbatar da cewa, masu gadin kofofin shiga rukunin sun yi iya kokarinsu na dakile farmakin, amma da yake 'yan fashin sun fi su yawa kuma suna dauke da makamai, hakan ya sa dole suka kira jami'an tsaro. Sai dai kafin jami'an tsaron su isa, 'yan fashin sun riga sun arce.
Wasu mazauna gidajen sun bayyana cewa wannan farmaki ya kasance karo na uku a cikin sati biyu. Sun ce a lokacin farmakin da ya gabata, 'yan fashin sun ji wa wasu rauni da kuma kwace dukiyoyi daga gidaje daban-daban a rukunin gidajen.
Har ila yau, mazauna gidajen sun jinjina wa jami'an tsaron 'yan sanda bisa kokarinsu na kawo dauki, duk da cewa koda yaushe 'yan fashin suna arcewa kafin isowarsu. Mazauna rukunin sun koka kan yadda babu ofishin 'yan sanda a cikin rukunin gidajen, tare da rokon hukumar 'yan sanda da ta samar da ofishin ‘outpost’ a wajen don tabbatar da tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu.
"Don Allah muna kira ga hukumar 'yan sanda su kawo mana dauki, ko da 'outpost' ne su aje mana, domin idan bata-gari suka san akwai 'outpost,' ba za su rika cin karensu ba babbaka ba," in ji wani mazaunin.