Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yafe wa wasu ɗaurarru da ke zaman waƙafi a gidan yarin Gusau, su 31.
- Katsina City News
- 20 Oct, 2024
- 375
A Juma'ar nan ne gwamnan ya kai ziyara gidan gyaran hali (gidan yarin) da ke Gusau, in da kuma ya sanya aka saki ɗaurarrun, kamar yadda kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada
A cikin wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu yau a Gusau, ya bayyana cewa gwamnan ya yanke shawarar yin haka ne bisa natsattsen binciken da aka gudanar game da waɗannan masu zaman jarun.
Sanarwar ta ƙara haske da cewa tsarin mulki ya ba gwamnoni da damar sassauta zaman yari da ma yafewa ga wasu.
Cikin jawabin da ya gabatar a wurin sanya hannu a wannan yafiya, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ɗaurarru ne masu laifuka daban-daban aka yafe masu domin a ƙarfafa masu gwiwa na su zama 'yan ƙasa nagari masu bin doka da oda.
“A yau na aiwatar da ikon da kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999, sashe na 212(1) ya ba ni, wanda ke da nufin yaye duk wani ƙunci da damuwa ga masu zaman jarun.
“An yanke wannan shawara ne bayan zuzzurfan binciken da aka yi game da waɗannan ɗaurarru, wanda kuma ya tabbatar da da-na-sanin su bisa abin da suka aikata a baya.
“Bugu da ƙari, na amince a bai wa kowanne daga cikin su N50,000 don su samu abin dogaro bayan fitar su cikin jama'a.
“Wannan yana daga cikin ƙoƙarin gwamnati na na rage cunkoso a gidajen yari, musamman a wannan lokacin da muke yawan kamo 'yan bindiga da masu ba su labaran sirri.”
Bayan zagaya cikin gidan yarin, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin bayar da taimakon da ya wajaba ga gidan na Gusau.
Tun farko a nasa jawabin, shugaban Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta jihar Zamfara, Dr. Umar Galadima, ya jinjina wa Gwamnan ne bisa ziyarar da kai, tare da yafe wa ɗaurarrun.