TATSUNIYA: Labarin 'Yar 'Autar Da Kogin Rantsuwa
- Katsina City News
- 07 Oct, 2024
- 360
Ga ta nan, ga ta nanku.
Akwai wani mutum mai mata ɗaya da ‘ya’yansa tara maza waɗanda yake ƙaunar su ƙwarai. Kowanne lokaci idan ya tafi kasuwa, sai ya sayo kifaye tara domin yaran nan. Sun ci gaba da zama cikin annashuwa har wata rana da ya kai kifayen gida, sai ‘yar autar gidan ta ɗauki ɗaya ta ci ba tare da ta tambaya ba. Ta aikata haka ne saboda wautar kuruciya. Da ya lura cewa kifayen sun yi ƙaranci, sai ya ce a tafi rafin Tantafane domin a gano wanda ya ci kifin.
Da suka isa rafi, babbar cikin yaran ta fara waka tana cewa:
"Kogi, kogin Tantafane,
In ni na cinye kifin baba,
Ruwa ka tafi da ni,
Karka dawo da ni."
Sauran yaran suka bi bayan ta, suna waka daya bayan ɗaya har su takwas, amma babu wanda ruwa ya tafi da shi. Sai kawai 'yar autar gidan ta rage, tana nan gefe tana shirme irin na yarinta. Daga nan, 'yan'uwanta suka matsa sai ta yi waka. Har suka ce idan ba ta yi ba, za su kashe ta.
Ta shiga cikin ruwa, ta fara waka tana cewa:
"Kogi, kogin Tantafane,
In ni na ci kifin baba,
Ruwa ka tafi da ni."
Da take cikin ruwan, nan take ‘yan ruwa suka janye ta. Ashe akwai wata tsohuwa da ta saba zuwa rafi domin kamun kifi, ita ce ta ƙi barin ‘yan ruwa su cinye 'yar autar saboda ta ga cewa tana da kyau. Saboda haka ta rike ta kamar ɗiyarta.
Bayan lokaci, 'yar autar ta girma har ta fara samun waɗanda suke neman aurenta. Sai dai tsohuwar nan ta yi mata tanadi, ta zabi ɗaya daga cikin manemanta. Sai tsohuwa ta ce masa ya kawo buhun kwarkwata a matsayin sadaki. Yaron ya kai, kuma aka daura musu aure.
Bayan aurenta, ‘yar autar ta tare a gidan miji. Ashe angon nata ɗan'uwan mahaifinta ne, sai dai ta yi shiru ba ta faɗa ba. Duk lokacin da maza suka tafi gona, tana daka abinci tana waka tana cewa:
"In daki turmin gidanmu,
Tim, kwal, kwal.
A yau uwata,
Ta zama surukata.
Ubana ya zama surukina,
Kannena ne abokan wasana."
Wata tsohuwa da ke zaune a zaure tana jin wannan waka, sai ta gaya wa mutanen gidan abin da take ji. Wasu daga cikinsu suka labe suna saurara, har suka ji waka daga bakin 'yar autar. Da suka fito suka ce: "Ashe ke ce?" Sai ta amsa da cewa: "E, ni ce." Nan take suka rungume juna, kowa yana murnar ganinta. Daga nan aka manta da zancen aurenta ta ci gaba da zama cikin danginta.
Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa
1. Shugabannin nagari sukan hukunta wanda ya aikata kuskure ko da kuwa a cikin iyalansu ne.
2. Hukunta mai laifi ba zai hana shi zama mutum mai kirki ba.
3. Shiga cikin wata al'amarin ba tare da bincike ba yakan haifar da matsala.
4. Kwadayi shine hanyar shiga wahala.
5. Lokaci yana gyara abubuwa da zasu zo nan gaba.
Mun Ciro wannan labarin daga littafin taskar tatsuniya na Dakta Bukar Usman