PDP Ta Dakatar Da Shugaban Jam'iyya A Karamar Hukumar Katsina, Ibrahim Galadima Saboda Zarge-Zarge
- Katsina City News
- 27 Sep, 2024
- 559
Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP a karamar hukumar Katsina ya dakatar da Ibrahim Galadima, Shugaban Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar. An sanar da dakatarwar ne bayan taro da aka gudanar a ranar 26 ga Satumba 2024, inda aka yi zarge-zarge masu yawa a kan Galadima.
A cikin takardar dakatarwar, wanda Abba Ila Rafin Dadi, Shugaban Kwamitin ya sanya wa hannu, an zarge Galadima da laifuka da suka hada da kawo tarnaki ga mutuncin shugabannin yankuna, amfani da dukiyar jam’iyya ba tare da izini ba, da kuma karɓar kuɗaɗen da ba a amince da su daga cikin kungiyoyin jam’iyya.
An yanke shawarar dakatar da Galadima bisa ga Dokar Jam’iyyar PDP, Babi na 59, wacce ke ba wa jami’an jam’iyya na cikin gida ikon daukar matakan ladabtarwa ga masu laifi. Kwamitin ya jaddada muhimmancin tsari da ladabi a cikin jam’iyyar tare da kira ga dukkan mambobi su yi biyayya ga ka’idojin jam’iyyar na hadin kai, gaskiya, da aminci.
“Dole ne mu hada kai wajen gina jam’iyya mai karfi da hadin gwiwa, wacce za ta iya lashe zabe da kuma bautatawa ga bukatun mutanenmu,” in ji sanarwar.
An aika takardar dakatarwar zuwa ga Shugaban Jihar Jam’iyyar PDP a Katsina don daukar mataki na gaba. Inji sanarwar