Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna matuƙar jimamin sa game da ibtila'in haɗarin jirgin ruwan da ya faru a Ƙaramar Hukumar Gummi ta jihar.

top-news

Da sanyin safiyar ranar Lahadin da ta gabata ne wani jirgin ruwa mai ɗauke da mutum 40 ya kauce hanya, inda ya yi haɗari a kogin Bakin Kasuwa na yankin Uban Dawaki da ke Ƙaramar Hukumar Gummi. 

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa gwamnan ya siffata wanan haɗari da cewa, wani babban bala'o'i ne.

Sanarwar ta Sulaiman ta bayyana cewa tuni aka umurci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Zamfara (ZEMA) da ta gaggauta kai ɗauki don lalubo waɗanda abin ya rutsa da su.

“Mun wayi gari da wani mummunan labarin haɗarin jirgin ruwa a kogin Bakin Kasuwa da ke yankin Uban Dawaki na Ƙaramar Hukumar Gummi, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka 40.

“Gwamna Lawal ya umurci Hukumar bayar da agajin gaggawa ta (ZEMA) da ta hanzarta binciken yanayin haɗarin, don a san irin taimakon gaggawar da za a bayar. 

“Gwamnan ya kuma umurci Kwamishinan ma'aikatar bayar da tallafi da jin ƙai, ta tattara duk bayanan da suka wajaba don kai agaji ga Iyalan waɗanda abin ya shafa. 

“Gwamna Lawal kuma ya yi addu'ar Allah gafarta wa waɗanda suka rasa rayuwakan su, ya jajanta wa iyalan su, tare da bayar da tabbacin ɗaukar matakan kare aukuwar haka nan gaba