BINCIKE: Babu Gaskiya A Takardar Da Ke Alaƙanta Gwamnatin Zamfara Da ’Yan Bindiga
- Katsina City News
- 12 Sep, 2024
- 371
Daga Musa Muhammad
Wata tarkardar ƙage, wacce aka ce ta fito ne daga gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau, mai ɗauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abubakar Nakwada, ta yi iƙirarin cewa Gwamna Dauda Lawal ya bayar da umurnin a saki Naira Biliyan 1,378,000,000 ga wasu manyan shugabannin ’yan bindiga.
Hakazalika, takardar ta yi zargin cewa kafafen yaɗa labarai irin su Sahara Reporters, Jackson Ude, da sauran su sun amfana da waɗannan kuɗaɗe.
To amma yana da muhimmanci a fahimci cewa, dukkan waɗanda aka yi wa ƙazafi a cikin wannan takardar sharri, su ne waɗanda suka ɗauki labaran fallasa alaƙanta Bello Turji da Alhaji Bello Mattawalle, Ministan Tsaro, da badaƙalar Alhaji Bashir Hadejia da aka kama da laifin ɗaukar nauyin ta'addanci da safarar makamai da zinare da dai sauransu.
Wannan ne ta sa Sakataren gwamnatin Jihar Zamfara, Alhaji Abubakar Nakwada, yayin da yake mayar da martani kan wannan takarda, ya ce "Wannan takarda mara tushe ta alaƙanta gwamnatin Zamfara da kiran zaman lafiya da Bello Turji, wanda ya kasance sanannen shugaban ’yan bindiga ne ya yi.
Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta yi kakkausar suka, inda ta musanta yin sulhu da 'yan ta’adda, kuma ta jaddada cewa takardar, wani yunƙuri ne da aka ƙirƙira da gangan da nufin gurgunta ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na samar da tsaro.
Don haka a fahimci wannan labarin da cewa ƘARYA ce, kuma yaudara ce.
Ita ma jam'iyyar AAC ta Omoyele Sowore, wanda kuma shi ne mawallafin jaridar Sahararepoters, wacce kuma tana cikin waɗanda aka ce sun amfana da waɗannan kuɗaɗe, ta fito fili ta yi tofin Allah-tsine da ganin wannan takarda, wacce ta ce ƙarya ce tsagwaronta.
Ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam'iyyar ta AAC, wanda ya ke kuma shi ne shugabanta, Omoyele Sowore ya ce, "Ya wajaba a gare mu mu nusar da jama'a irin sabon salon farfagandar da Bola Tinubu ya fito da ita na zubar da mutuncin mani da mutunci, ni da SaharaReporters.
"Wata takardar cikin gida, wacce aka alaƙanta da Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, tana nan tana yawo a tsakanin jama'a, aka ce wai an ware wasu maƙudan kuɗaɗe don a raba wa 'yan ta'adda da wasu kafafen watsa labarai.
Sowore ya ce, wannan ƙarya ce, bai san da wani abu mai kama da haka ba.
Shi ma, ɗaya daga cikin waɗanda aka ambaci sunayen su a waccan ƙagaggar takarda, Jacson Ude, a shafin sa na tweeter (X), ya yi watsi da wannan batu, inda ya ɗora laifin kan tsohon Kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Bello Matawalle.
Jackson Ude ya yi zargin cewa Tsohon Kwamishinan yaɗa labaran, ya kasance ya ɓoye kansa a wani wuri, inda ba abin da ya ke yi sai ƙage-ƙagen ƙarairayi kan duk waɗanda suka ya ƙi gwammatin Matawalle.
Don haka ya ce, wannan takarda sam ba ta da tushe balle makama, ƙarya ce tsagwaronta.